Murtala Muhammad" />

Siyasar Daba A Kano: Bukatar A Yi Wa Tufkar Hanci

Kowa ya sani Gwamnan Jiha shi ne shugaban tsaro a jiharsa, kamar yadda bahaushe ke cewa duk jin dadin inuwar gemu bai kai ga makogoro ba. Toh haka batun yake, don duk jin dadin zaman lafiyar al’umma bai kai kamar yadda masu mulki ke ji ba. Sannan su ma sauran masu rika da mukaman siyasa, kama daga Sanata, ‘yan Majalisar Tarayya, ‘yan majalisar jiha da sauransu duk masu ruwa da tsaki ne, kuma alhakin tabbatar da wanzuwar zaman lafiya na rataye a wuyansu.

Idan ka waiwaya ba ya za ka ga cewa, a tarihin siyasar jihar Kano, duk gwamnonin da aka yi a baya tun daga Jamhuriya ta farko har zuwa yanzu Jamhuriya ta uku, an yi ta samun sabani a harkar siyasa a tsakanin jiga-jigan ‘yan siyasar jihar. Wanda a wasu lokutan za ka samu talakawa su ne ke kan gaba wurin yi wa kawunansu illa, ta hanyar kutsawa harkar rikici da dabar siyasa.

Bisa wannan dalilin ne ya sa na kuduri aniyar yin wannan rubutu, domin jan hankalin matasa da su kauracewa harkar daba. su fahimci yadda lamarin yake, da irin sarkakiyar da ake ciki.

Matasa ku farka domin ku ne shugabannin gobe, ku tuna za ku iya zama jami’an gwamnati nan gaba idan aka yi muku irin wannan halayyar da gwamnatin Kano ke nuna wa yanzu, ta wacce fuska zaku kalli abin, ku sani fa ita kujerar gwamnati kowacce iri ce, kamar damina take, idan rani ya zo, ko ka yi girbi amfanin gonar ya fadi, ko ka ki yin girbi, iska ta zo ta ture shi, to haka mukamin gwamnati yake, babu wani abu dawwamamme a cikin mukamin gwamnati.

Matasa ku ne kashin bayan kowacce al’umma, domin ku ne shugabannin gobe, ku yi tunani Sani Lawan Kofar mata, Musa Iliyasu Kwankwaso, ko Baffa Babba Dan’Agundi, yaya matsayin siyasar su take a jihar Kano, idan ka fassara su da macizai wadanda ba sa gidan kansu, wannan daidai ne, domin kowannensu babu gwamnatin da ba ta tafi da su ba, tun daga gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau, zuwa gwamnatin Kwankwaso mataki na biyu da yanzu kuma gwamnatin Mai Girma Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

Su fa wadannan mutane ‘yan kasuwar bukata ne kawai, basu san komai ba, fa ce kaska rabi mai jini, sun jingina da Gwamna Ganduje ne kawai domin yana da gwamnati, idan da bashi da gwamnati da babu wanda za a gani a cikinsu.

Su wadannan ‘yan siyasa, ‘yan siyasa ne na kasuwar bukata ko kuma kaska. Matasa ku guje wa irin wannan ta’addanci da ba zai haifar da da mai ido ba. Ku yi siyasa idonku a bude, ku fita batun zakalkalewa. Babu ruwanku da cusa kawunanku a cikin rikicin dake tsakanin Shugabanninmu ‘yan siyasa, domin kuwa sun fi kusa, suna iya shiryawa su zama aminai a yau din nan.

Shugabanninmu ‘yan siyasa suna bayar da gudunmawa dari bisa dari a duk wata harkar siyasar matasa, walau dabi’a ce ko hali. Sannan Shugabanni ‘yan siyasa su ne idan sun so, saboda son ransu za su haddasa gaba tsakanin matasan da suke ginshikin al’ummar wannan yanki namu.

Irin wannan ta’annuti na Sara suka da rashin mutunci, ba za a ce kaitsaye laifin wani mutum guda bane, domin kuwa su matasan da ake amfani da su wurin aiwatar da lamarin sun fi kowa rashin hankali da rashin sanin ciwon kai.

Sannan a bangaren jami’an tsaro kuma, ya kamata su kwana da sanin cewa su fa ma’aikatan gwamnati ne ba ‘yan siyasa ba. Ya kamata rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta sa wando daya da duk wani aikin daba da sunan siyasa ko wani abu makamancin hakan.

Ina kira da babbar ga masu ruwa da tsaki a Kano, ku sani Kacokaf zaman lafiya ya dogara ne ga kokarinku, yana daga cikin aikinku kare rayuwa da dukiyoyin al’umma. ‘Yan Siyasa ku ji tsoron Allah, ku yi abin da aka zabe ku da ku yi, kuma ku kasance masu biyayya ga dokoki da tsarin mulkin kasa.

Exit mobile version