Daga Nasir S. Gwangwazo, Abuja
Tun gabanin shekara ta 2018 ta kama daga dukkan alamu siyasar jihar Kano ta fara kamawa da wuta, inda sanata mai kula da Kano Ta Kudu kuma tsohon gwamnan jihar, Alhaji Kabiru Gaya, da tsohon dan majalisar tarayya kuma wakilin mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin majalisar wakilai, Alhaji Kawu Sumaila, su ka saka zare.
Da yawan mutane sun a daukar cewa, rikicin na kwanan nan ne lokacin da Kawu Sumaila ya yiwa Sanata Gaya tonon silili a kafafen yada labarai na Kano cewa, a matsayin sanatan na shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisa ya rage kudin da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta ware, don cigaba da aikin titin Kano zuwa Maiduguri, lamarin day a ce ya sanya Buhari mummunan bacin rai a lokacin da ya ke jinya a Turai.
To, amma ashe amma a zahirin gaskiya ba kwanan nan a ka soma wannan rigima ba. Ta samo asali ne tun gabanin manyan zabukan 2015, inda Kawun ya ke zargin Gaya da yi ma sa dungu a lokacin da tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, a ke zargin ya yiwa shi Kawun manakisar tsayawa takara a wancan lokacin, inda ya yi biyu-babu; bai koma majalisar wakilai ba, bai samu takarar gwamna ba kuma sannan ba a ba shi takarar mataimakin gwamna ba.
To, amma bayan da mai ‘takalmin karfe’ ya ballatsewa Kawu, sai a ke zargin cewa Gaya ya ki yarda ya juya wa Kwankwaso baya tunda shi an riga an dawo ma sa da takararsa ta sanata, amma shi Kawu a ka hana shi komawa mukaminsa na dan majalisa.
Bayanai sun nuna cewa, tun daga wannan lokaci ne Hon Kawu ya kullaci Sanata Gaya, kuma ya yanke shawarar neman kujerarsa a zaben 2019 mai gabatowa.
Wakilinmu ya nemi jin ta bakin sanatan da kuma tsohon dan majalisar, amma hakan ya ci tura, saboda majalisa tan a hutu. Amma idan da hali za mu cigaba da bibiyar batun.