Siyasar Katsina: An Fara Zare Ido Kan Neman Kujerar Gwamna

Gwamna

Tare Da El-Zaharadeen Umar, 

Ya zuwa yanzu an fara kada gugen siyasa, a tarayyar Nijeriya hakan ta sa jihar Katsina ta fara daukar dimi a siyasance domin gane inda aka dosa a zaben 2023 mai zuwa, wanda suke ganin shi ne mafita a wannan yanayi da ake ciki.

Shakka babu jihar Katsina ta bi sahu wajan samar da zazafan yanayin siyasa wanda yanzu haka ido ya fara ja wajan gani wanene magajin gwamna Aminu Bello Masari a zabe mai zuwa,

Yanayin babu kyau, domin akwai masu san mulki  kamar rayuwarsu, kai sun ma fi fifita mulkin akan rayuwarsu, domin wasu abubuwan da suke yi kai kasan babu lisafin mutuwa a ciki balanta lahira ko hisabi da sauran su.

A hankali al’amari ya fara, sai dai yanzu ya koma baba a ya yin da aka fara karo da juna akan neman kujerar gwamnan jihar Katsina wanda gwamna mai barin gado yace ba shi da dan takarar da zai tsaida domin ya gaje shi.

Yin wannan magana ya haifar da rudu da shiga firgici a tsakanin masu neman mulkin wanda yanzu haka wasu kamar an yi masu allura, sun dage wajan ganin makomarsu ta yi kyau koda ba su samu kujerar gwamna ba.

Sai dai masu sharhin siyasa suna ganin wannan kalaman na gwmana Masari tamkar wani basaja ne saboda mafiyawan masu neman takarar sun sakankace da cewa gwamna Masari na iya daukar wani daga cikin su ya tsayar da shi sannan ya goya masa baya.

To an sha baban, domin kuwa yanzu yaki ya koma ga masu karfin neman jama’a domin kafa tsanin samun takarar gwamnan jihar Katsina a karkashin jam’iyyar APC a zabe mai zuwa.

Bincike ya nuna cewa masu neman takarar kujerar gwamna a karkashin jam’iyyar APC a jihar Katsina sun kai goma wasu ‘yan Abuja ne wasu kuma suna cikin wannan gwamnati ta jihar Katsina, wasu kuma ba su rike da kowane irin mukami.

Wannan yasa ake ganin al’amari ya zama wane yaro, ya koma ga mai rabo kan samu marar rabo sai kallo, alamu na nuna cewa za a samu turjiya wajan samun daidaiton wanda zai tsaya takara duba da irin kalaman da gwamna Masari ya yi na cewa bashi da wan zai goyawa baya sai wanda jama’a suka zaba.

Haka tasa, wasu ke tambaya cewa haka Masari zai bar jam’iyyar ta fada hannun masu neman abokan mutuwa su mutu tare da jam’iyyar? Ko ko dai irin abin nan na ‘yan siyasa na wasa da hankali mabiya, sai an yi can ruuu sai kuma a dawo nan raaaa.?

Amma dai koma menene lokacin ya zo, abinda kawai ya rage shine, inda aka dosa, da kuma yadda zata kare idan wasu sun rasa domin lallai sai haka ta faru, shin za su tsaya a nemi nasara ko za su kama gaban su kamar yadda suka yi kafin yanzu?

Kazalika wannan yanayi ya samar da wasu bangarori a tsakanin masu neman takarar inda ake hangen wasu sun shirya wasu kuma daman wasa suke, saboda an samu labarin daya daga cikin masu neman wannan kujera ya rikice ya fadi kasa saboda maganar da gwamna Masari ya yi ta cewa bashi da dan takara.

Abinda wasu ke ganin daman bai cancanta ba, yana neman ya shige rigar gwamna Masari a tsaida shi takara yadda za a yi saurin faduwa, amma yanzu za a gane inda ya sa gaba, to in ba haka daga cewa gwamna bashi da dan takara sai ka yanke jiki ka fadi.

Sannan shi wannan dan takara ya yi kaurin suna wajan dukule hannunsa akan jama’a shi yasa ake ganin daman can bai cancanci tsayawa kowace takara ba, sai dai son zuciya irin ta dan adam da kuma neman mulki babu gaira babu da dalili.

Yana kallon kaisa wani mutun mai dadadiyar siyasa da kuma biyaya inda har yake ikirarin cewa yafi kowa cancantar ya zama gwamnan jihar Katsina bayan gwamna Masari ya kammala wa’adin mulkinsa.

Ammai dai wasu na ganin abin da wahalai wai gurguwa da auran nesa, a tarihin siyasar jihar Katsina babu wanda ya samu dama kamar shi, amma kuma babu wanda yaki amfani da ita kamar shi, ya zuwa yanzu, ya kasa maida mutun goma mutune a siyasar jihar Katsina.

Har gobe ba a san wani kokari da ya yi ba wajan gine jama’a da samar masu ayyuka da nema masu mukami a cikin wannan gwamnatin, amma ya kuma daga gefe guda yana son lallai sai an tsaida shi takarar gwamna.

Wasu na mamaki ganin wannan mutumin da irin wannan shige da fice a maimakon ya koma gefe tunda an shaidai shi da rashin iya siyasa, kai har yanzu da aka kada guguwa siyasa, karamar hukumarsa ba a hannunsa take ba.

Haka kuma wasu na nan suna jiran wani attajiri ya tsayar su takara domin su ci a bagas, sai dai wannan attajiri yana fuskantar kalubalan talakawa saboda yadda ya yi kaka gida a wannan gwamnati ya hanata motsawa da kawo mata cikas.

Wasu na ganin wannan attajiri a matsayin wata gawurtacciyar annoba a siyasar Katsina, sai yanzu aka gano da dalilin da yasa tsohon gwamnan jihar Katsina Ibrahim Shehu Shema yasa kafar wando daya da shi, baya da imani ko kadan.

Duk wani hali da jihar katsina ta shiga ana zargin yana daga cikin wadanda suka taimakawa wajan faruwar haka, sai dai kaiwa an fi ganin laifiingwamna Masari tunda shi ke biye masa wajan biya masa bukatarsa ta siyasa.

Bisa wannan da ma wasu dalilin yasa jama’a ke tsoro da firgicin kadda Allah ya kawo ranar da zai tsaida dan takarar gwamnan a jihar Katsina domin hakan zai kara ba shi dama wajan kara baje kolinsa a gwamnatance tare da rike makogwaron duk wanda zai zama gwamna a 2023.

Kodayake kasan ‘yan siyasa wani lokacin suna manta lissafin, duk wani al’amari na su baka ganin an sanya mutuwa a ciki domin ita ce kadai ke saurin canza abu daga yadda yake ba tare da sanin ko tsammani ba.

Duk wadannan abubuwa da suke tunani, sai fa idan rayuwa ta kai, amma idan aka samu akasin haka, to anan ne dibara ke kwace masu wani lokaci, sai ka ga an yi lissafi amma ba Allah a cikin lissafin, sun fi fifita na su a kan kaddarar Ubangiji.

 

Exit mobile version