Kasar Amurka ta ce wasu Dakarunta gwanayen jefa bama-bamai tare da rakiyar wasu jiragen yaki sun ratsa gaban tekun kasar Korea ta Arewa tun Asabar domin nuna mata irin karfin soja da Amurka ta mallaka.
Dana White kakakin ma’aikatar Tsaro ta Amurka ta bayyana cewa kewayen da dakarun Amurka su ka yi don nuna karfin sojan da za su iya yin duk abin da ake so ne.
Ta bayyana cewa kasar Amurka na shirye domin amfani da karfin soji domin ganin ta kare gida Amurka da kawayenta.
A halinda ake ciki, wasu bayanai na cewa an sami ‘yar girgizan kasa kusa da inda Korea ta Arewa ta yi gwajin makami mai linzami bada dadewa ba.
A lokacin da aka bashi dama domin jawabi Ministan Waje na Korea ta Arewan Ri Yong-Ho ya ce shugaban Amurka tababbe ne kuma mai son iyawa.
Ya bayyana cewa ikirarin da Donald Trump ya yi cewa zai daidaita Korea ta Arewa, ya sa suka kintsa rokokin su domin gano komi na sirrin Amurka.