Muhammad Maitela" />

Sojan Sama Sun Tarwatsa Sansanin Boko Haram A Borno

Jirgi

Rundunar sojojin saman Nijeriya (NAF), a da ke aikin samar da tsaro a karkashin rundunar ‘LAFIYA DOLE’, ta bayyana samun nasarar kai samame a mafakar bangaren kungiyar Boko Haram wadda aka sani da ‘Islamic State of West Africa Probince’ (ISWAP) a arewacin jihar Borno.
Commodore Ibikunle Daramola, kuma Daraktan yada labarai na rundunar sojan saman ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwar manema labarai, a ranar Talata, a biyo bayan wani samamen hadin gwiwa da ta kai a mafakar mayakan, ranar Litinin.
Daramola ya kara da cewa, sojojin saman sun yi nasarar halaka wasu daga cikin shugabanin ISWAP tare da mayakan ta a kauyen Magari da ke zirin Tafkin Chadi a arewacin jihar Borno.
Har wala yau kuma, ya yi karin hasken cewa, sun kai samamen ne baya ga cikakken rahoton bayanan sirri da suka samu, wanda ya tabbatar musu kan cewa kwamandojin kungiyar ISWAP sun tattaru a yankin tare da sauran mayakan su.
“samamen ya zo ne bayan gudanar da binciken kwararru a karahen wannan mako, dangane da kai-komon manyan kwamandojin kungiyar ISWAP a wurare guda biyu dake yankin- inda rahoton da ya tabbatar mana da kasancewar manyan ahugabanin kungiyar a wajen”.
“wanda a cikin shiri, mun yi amfani da jiragen yakin rundunar sojan sama guda biyu; samfurin ‘Alpha Jet’ tare da hadin gwiwa da (ISR), inda muka tsara yadda samamen zai gudana a wadannan wurare da keyankin”.
“yayin da ta sama muka auna iya inda muke da nufi, tare da saita inda manyan kwamandojin mayakan suke, muka sake musu wuta”.
“wadannan bama-bamai da muka cilla daga jiragen yakin nan guda biyu, sun dira daidai wurin da muka saita su dinka, inda kan ka ce me, sun tarwatsa wajen; lamarin da ya jawo wurin ya turnuke da wuta”.
“yan kungiyar da dama ne suka kwanta dama a lokacin wannan samame”. Ya nanata.

Exit mobile version