Connect with us

LABARAI

Sojin Nijeriya Sun Kama Wadanda Ake Tuhuma Da Kai Wa ’Yan Boko Haram Man Fetur

Published

on

Rundunar Sojin Nijeriya ta ce ta kama wasu mutane biyu da take zargi da yi wa ‘yan Boko Haram safarar man fetur a wani wuri da ke Nafada, ta Jihar Gombe.
Kakakin rundunar, Tedas Chukwu, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.
Ya ambata sunayen mutanan da, Mohammed Adamu Zika, wanda direban mota ne, da kuma, Bukar Adamu Haji, wani mataimakin manajan wani gidan sayar da man fetur a yankin.
Mista Chukwu ya ce, wani da suke yin aikin tare da shi ya tsere, amma dai Sojin rundunar suna kokarin kama shi.
“Mutane biyun da ake tuhuman suna amsa tambayoyi a yanzun haka, bayan nan ne kuma za a gabatar da su ga hukumomin da suka dace domin hukunta wa,” in ji shi.
Mista Chukwu, ya bayyana cewa, rundunar ta rigaya ta gargadi dukkanin gidajen sayar da man da ke yankin na Nafada, da su guji sayar da mai mai yawa ga masu motoci.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: