Sojoji Na Bukatar Addu’ar Ganin Bayan ‘Yan Ta’addan Boko Haram – Janar Abimbola

’Yan Ta'adda 16

Daga Sulaiman Ibrahim

Wani Janar na Sojan Nijeriya, Brig.-Gen. Abimbola Yussuph, a ranar Lahadi ya nemi addu’a sosai ga sojoji don samun nasara a yakin da suke yi da kungiyar Boko Haram, ‘yan bindiga da sauran masu tada kayar baya.

Da yake amsa tambayoyi ga manema labarai a Abuja yayin bikin cikar shekaru uku da hidimar Temple of Mercy Prophetic Ministry, ya ce yakin da ake yi da masu tayar da kayar baya ya kai matakin da ya kamata a hada da addu’o’i.

Ya ce: “Ko a yaki, akwai wasu matakai na ruhaniya saboda sojan da ke yakin nan yana da imanin da ya kulle a zuciya, kuma duk abin da ya yi imani da shi, ana da bukatar karfafa mashi gwiwa, don bashi damar cigaba da yakin.

“Don haka, zan ce muna bukatar wannan bangaren na ruhaniya don ci gaba da yaki kuma na sani, da rahamar Allah, za mu ga karshen wannan yaki, domin kowane yaki yana da karshe.”

A nasa bangaren, shugaban cocin, Akin Akinnigbagbe, ya roki shugabannin Nijeriya da su ji tsoron Allah.

Exit mobile version