Rundunar Sojojin Nijeriya ta ƙaryata rahotannin da ke yawo cewa ƴan bindiga sun mamaye sansanin Sojoji tare da sace manyan bindigogi guda shida (GPMG) da alburusai sama da 30,000 a Obanla, jihar Kwara.
A cikin wata sanarwa da Mataimakin daraktan hulɗa da Jama’a na runduna ta 2, Laftanar Kolo Polycarp Okoye, ya fitar, ya bayyana cewa rahoton da ke yawo a yanar gizo ba gaskiya ba ne.
- Kotu Ta Kori Buƙatar Minista Tinubu Na Hana Fitar Da Takardun Karatunsa
- Uwargidan Shugaban Ƙasa, Remi Tinubu, Ta Nuna Damuwa Kan Ƙarancin Malamai A Duniya
Ya ce: “Sojojin Bataliya ta 148 (Rear) suna gudanar da aikin ƙarasa kakkaɓe sansanonin ƴan ta’adda a jihohin Kogi da Kwara, kuma tuni sun kai iyakar Kwara–Ekiti, inda suka kashe ƴan bindiga biyu tare da kwace bindigogi AK-47 guda biyu sabbi.”
Okoye ya ƙara da cewa: “Babu wani lokaci da sansani ko makamai Sojojin ya shiga hannun ƴan ta’adda, kamar yadda wasu kafafe suka yaɗa. Wannan labari ƙanzon Kurege ne da aka shirya don ruɗar da jama’a da kuma rage ƙwarin gwuiwar jarumai da ke aiki tukuru don dawo da zaman lafiya a yankin.”
Ya tabbatar da cewa Rundunar Sojojin Nijeriya za ta ci gaba da murƙushe duk wani irin aikata laifi a sassan ƙasar nan.
Har ila yau, ya roƙi jama’a da su yi watsi da wannan rahoton ƙaryar kuma su ci gaba da baiwa jami’an tsaro goyon baya ta hanyar samar da sahihan bayanai da za su taimaka wajen nasarar ayyukan Soji.