Sojan Nijeriya a jihar Katsina sun yi nasarar hana wani harin da ‘yan ta’adda suka shirya kan mutane a hanyar Kurfi-Batsari da sanyin safiyar ranar Laraba, 18 ga Yuni, 2025.
Maharan sun fara harin da karfe 5:00 na safe, amma Sojoji suka farmaki su wanda hakan yasa suka kara gudu, inda yayin musayar wutar suka kashe ‘yan ta’adda takwas tare da kwato manyan bindigogi AK-47 da harsasai masu yawa.
Duk da cewa wani Soja ya samu rauni a artabun, an kai shi asibiti don samun kulawa, kuma yana cikin kwantar da hankali.
Hukumar ta yaba wa jaruntakar Sojojin da kuma goyon bayan al’ummar yankin, wanda ke taimakawa wajen inganta tsaro.
“Wannan nasarar ta nuna mahimmancin ci gaba da lura da kuma haɗin gwuiwa tsakanin Sojoji da jami’an tsaro. Ya zama dole kowa ya taka rawarsa wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar Katsina,”
In ji kakakin birgediyar