Sulaiman Ibrahim" />

Sojoji Sun Farmaki Mahakar Ma’adanai A Zamfara, Sun Cafke ‘Yan Bindiga 150

Rundunar Sojojin Operation Sahel Sanity sun gudanar da wani samame na musamman kan wata cibiyar hakar ma’adinai wacce ta ratsa hanyar Gadan Zaima a karamar hukumar Bukuyyum ta jihar Zamfara, a inda aka samu nasarar kama wasu mutane 150 da ake zargin ‘yan garkuwa da mutane ne, in ji Daraktan Yada Labarai na rundunar, Birgediya Janar Benard Onyeuko.

“A yayin samamen da aka kai wajen mahakar ma’adinan, wanda wurin ya kasance wani shinge ne ga masu garkuwa da mutane, sojojin sun gano bindigogin Dane guda 20 kirar hannu. An harbe Daya daga cikin wadanda ake zargin yayin da yayi yunkurin tserewa.
“Cikin dan karamin bincike na matakin farko da aka gudanar, sakamakon ya nuna cewa, hako ma’adinai ba bisa ka’ida ba yana lalata tattalin arzikin kasa, kuma ana amfani da kudaden da ake samu wajen daukar dawainiyar ta’addanci da ‘yan ta’adda.
“Hakanan kuma, sojoji dake sintiri akan hanyoyi, sun gamu da wasu ‘yan bindiga uku a kan babura a kusa da kauyen Maigalma cikin karamar hukumar Anka ta jihar Zamfara wadanda ke kokarin kai hari kan mazauna gari da ba su ji ba su gani ba.
“Daya daga cikin ‘yan bindigan an harbe shi, biyu sun tsere yayin artabunsu da sojoji. Sojojin sun kwace bindiga kirar AK-47 guda daya, cike da bullet mai nauyin 7.62mm, da kuma babura biyu daga hannun barayin, ”Janar Onyeuko ya kara bayyana hakan.
Ya ce wani tubabben shugaban ‘yan bindiga mai suna Bornon Kejo ya mika kansa ga sojoji ya kuma mika wasu bindigogin AK-47 biyu da abun zuba harsashinsu guda biyu a Zurmi da ke karamar hukumar Zurmi ta jihar, ya kara da cewa ana ci gaba da kokarin dawo da makamai dake hannun ‘yan bindiga tare da karfafa ma wasu kwarin gwiwar rungumar zaman lafiya tare da mika makamansu.
Ya kuma ce, “A cikin wannan karon, an kama manyan motoci bakwai dauke da shanu wadanda ake zargin cewa na ‘yan bindiga ne a kan hanyar Jibia-Katsina da kuma hanyar Gusau-Zariya,” in ji shi.

Exit mobile version