Rabiu Ali Indabawa">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home LABARAI

Sojoji Sun Fatattaki Boko Haram A Mahaifar Tsohon Gwamnan Yobe

by Rabiu Ali Indabawa
February 15, 2021
in LABARAI
2 min read
Sojoji Sun Fatattaki Boko Haram A Mahaifar Tsohon Gwamnan Yobe
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

A jiya da maraice ne wasu da ake zaton mayakan Boko Haram ne suka kai hari mahaifar tsohon Gwamnan Jihar Yobe, Ibrahim Gaidam, dake garin Gaidam a shiyyar Arewa maso Gabashin Nijeriya, sai dai al’ummar garin Gaidam sun ce maharan ba su sha da dadi ba a wajen jami’an tsaro ganin yadda aka fattatake su, wasu maharan sun arce da harsahin bindiga a jikinsu.

Wasu mazauna garin Gaidam sun ce harin na jiya shi ne na cikon takwas a cikin watanni 13 da maharan ke kai wa garin, amma duk harin nasu basu ci nasara ba. Tun da misalin karfe biyar na yammacin jiya ne suka fara jin harbe harben bindiga, lamarin da ya takaita harkokin jama’a kowa ya shige gida, amma har kusan goma sha biyu na dare ana jin karar harbe harbe.
Bayanai daga garin Gaidam na nuni da cewa mayakan sun yi awon gaba da wasu ma’aikatan kwastam guda uku, amma babu wani karin haske daga vangaren hukumomin kwastam din.
Mai magana da yawun jami’an ‘yan sandan jihar Yobe Abdulkarim Dungus ya tabbatarwa Muryar Amurka da aukuwar wannan lamari duk da cewa ya ce bai ji daga vangaren Kwastom ba, amma rahotanni da suke samu daga wurin jami’an su sun shaida musu hakan.
Dungus ya ce “wannan wani harin ba-zata ne suka kai ba kamar yanda aka saba gani, sun shigo ne farat daya suka fara bude wuta, inda sojoji suka fito suka yi artabu da su, har ma jirgin yakin sojoji ya kawo dauki domin fatattakar maharan.”
Ya ce duk da haka maharan sun yi nasarar fasa shaguna daya zuwa biyu wanda har yanzu ba a iya tantance adadin shagunan da aka fasa ba, sai kuma batun awaon gaba da ma’aikatan kwastam guda uku kana babu wani rahoto a kan ko wani ya mutu ko kuma wani ya samu rauni, kana ba a yi kone-kone kamar yanda suka saba ba.
Wasu mazauna garin na Gaidam sun fadawa wakilin Sashen Hausa yanda al’amarin ya faru. Sun tabbatar da babu wanda aka jiwa ciwo haka zalika babu wasu kone-kone da ‘yan ta’addan suka yi. Sai dai wasu ‘yan ta’addan sun samu munanan raunuka daga fatattakar da sojoji suka musu.
A wani labari na daban, Akalla sojojin Nijeriya uku rahotanni suka ce mayakan ISWAP sun kashe a wani harin kwanton vauna a Borno. Wata majiyar sojin Nijeriya ta tabbatar wa kamfanin dillacin labarai na AFP da kai harin, inda ta ce akwai sojoji biyu da suka vata a harin da aka kai da yammacin jiya.
Majiyar ta ce mayakan ISWAP sun bude wa ayarin sojin Nijeriya wuta ne a kauyen Barwanti da ke yankin Tafkin Chadi bayan daya daga cikin motar ayarin na sojojin ta taka nakiya da ‘yan bindigar suka dasa.
An kai wa ayarin sojin na Nijeriya hari ne yayin da suke kan hanyar zuwa Baga.
ISWAP da Boko Haram na ci gaba da zama barazana a yankin Arewa maso Gabashin NIjeriya, inda suka kashe dubban mutane tare da raba miliyoyi da gidajensu.

SendShareTweetShare
Previous Post

Ya A Ke Gane Mugu?

Next Post

Okonjo-Iweala Ce ‘Yar Afirka Ta Farko Da Za Ta Jagoranci Hukumar Cinikayya Ta Duniya

RelatedPosts

Naira

Naira Na Shirin Sake Faduwa Warwas – FMDQ

by Rabiu Ali Indabawa
6 hours ago
0

Za Ta Iya Kai Wa Dala 500 Cikin Mako Mai...

Ruwan Sha

Gwamnatin Bauchi Na Shirin Raba Tsaftacaccen Ruwa Sha Lita Miliyan 75 Kullum

by Rabiu Ali Indabawa
6 hours ago
0

Daga Khalid Idris Doya, Hukumar Samar da Tsaftacaccen Ruwa ta...

Sarakuna

Sarkin Gwandu Ya Bukaci Sarakunan Gargajiya Su Bauta Wa Al’umma

by Rabiu Ali Indabawa
6 hours ago
0

Daga Umar Faruk, Mai Martaba Sarkin Gwandu, Alhaji Muhammadu Iliyasu...

Next Post
Okonjo-Iweala Ce ‘Yar Afirka Ta Farko Da Za Ta Jagoranci Hukumar Cinikayya Ta Duniya

Okonjo-Iweala Ce 'Yar Afirka Ta Farko Da Za Ta Jagoranci Hukumar Cinikayya Ta Duniya

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version