Umar A Hunkuyi" />

Sojoji Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda 39 A Jihar Zamfara

Akalla ‘yan bindiga 39 ne Sojoji suka kashe a wasu farmaki biyu da Sojojin suka kai a Zamfara, a wannan makon.

kakakin rundunar, Operation Hadarin Daji, Kaftin Oni Orisan, ne ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Asabar, ya ce an gudanar da farmakin ne a sassan Bakura da Anka na Jihar.

A cewar shi, 19 daga cikin ‘yan bindigar an kashe su ne a wata arangama da suka yi da Sojojin a dajin Anka, sa’ilin da guda 20 aka kashe su a Bakura.

Orisan ya nanata kudurin da rundunar Sojin ta dauka na cewa ba za ta kai hari a kan duk wani dan bindigar da ya tuba ba.

Sai dai ya ce, wadanda suke tubabbun amma sukan dauki bindigogi suna tafiya a cikin tawaga za a dauke su a matsayin abokan gaba ne.

Ya shawarci tubabbun ‘yan bindigar da su mika makaman su ga hukumomin da suka dace su rungumi shirin zaman lafiya na gwamnatin Jihar.

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya bayar da rahoton da ke nuni da cewa, tun daga lokacin da aka kaddamar da shirin zaman lafiyar a Jihar watanni biyar da suka gabata, an sami zaman lafiya a sassan Jihar.

Exit mobile version