Dakarun runduna ta 6 ta sojojin Nijeriya mai taken ‘Operation Lafiya Nakowa’ sun yi nasarar kashe ‘yan ta’adda biyu tare da kwato tarin makamai da alburusai a karamar hukumar Takum dake jihar Taraba.
Wannan farmakin na daya daga cikin kokarin da sojoji suke yi na kawar da ‘yan ta’adda da miyagun ayyuka a fadin jihar.
A wata sanarwa da mukaddashin daraktan hulda da jama’a na rundunar soji ta 3, Aliyu Danja a Jalingo ya fitar, rundunar ta 6 da rundunar sashe ta 3 ta ‘Operation Whirl Stroke’ ne suka gudanar da harin.
Danja ya ce, sojojin a yayin da suke aiki da sahihan bayanan sirri dangane da shirin kai hari kan al’ummar Chanchangi da kungiyar ta’adda ta Bojo ke shirin yi a ranar 15 ga Satumba, 2025, sun yi artabu da ‘yan ta’addan a kan hanyar Demeva zuwa Chanchangi.