Kwamandan rundunar sojoji mai taken (Operation Lafiya Dole), Manjo janar Ibrahim Attahiru, ya kaddamar da sabbin dabarun yakar kungiyar Boko Haram yau Talata a barikin soji na Maimalari dake Maiduguri.
Kwamandan ya ce, ‘an kaddamar da rundunar ne, don kirkiro da sabbin dabarun yaki da masu tada kayar baya ke yi a jihar da kasa baki daya.
Attahiru, ya kara da cewa, ‘rundunar sojin da aka horar kwararru ne a dabarun yaki da ta’addanci, don haka za a tura su, don murkushe masu tada kayar bayan.
‘A kokarinmu na kawo karshen ‘yan kungiyar Boko haram, mun tabbatar da sojojin sun samu horo da kayan aiki na musamman’, inji Attahiru.