Sojoji Sun Kama ’Yan Kungiyar Asiri 23 Da Masu Lalata Bututun Mai 15

Rundunar Soji ta 81, a ranar Asabar, ta kama mutane 23 wadanda ake kyautata zaton ‘yan kungiyar asiri ne, wadanda suke yin wani atisaye na shigar da sabbin shiga kungiyar ta su ta yin fashi da makami da sace mutane.

Sojojin sun kuma ce, sun kama wasu mutanan 15 da ake kyautata zaton masu lalata bututun mai ne, sun kuma gano manyan jarkokin man shake da man na Fetur har guda 31 a tare da su.

Kwamandan runduna ta 81 na rundunar Sojin, Manjo Janar Enobong Udoh, ne ya bayyana hakan a wani taro na 174 na bataliyar da ya gudana a Ikorodu, ta Jihar Legas.

Kwamnadan wanda Birgediya Janar Moundhey Ali, ya wakilce shi, ya ce, dukkanin mutanan da suka kaman sun kama su ne a wurare daban-daban, ya kara da cewa, tsananta binciken da suka yi da kuma labaran sirrin da suka samu ne ya taimaka masu yin kamun.

“A ci gaba da farmakin da muke kaiwa batagari da ‘yan kungiyar asiri a ciki da wajen Legas, har zuwa Jihar Ogun, dakarunmu na bataliya ta 81 sun kama mutane 23 da ake kyautata zaton matsafa ne a Ikorodu, ranar 16 ga watan Afrilu.

Sama da ‘yan kungiyar asiri 150 na, “Eiye” sun taru suna gudanar da wani taron atisaye na sirri domin daukan sabbin shiga kungiyar da kuma yin shirin kaddamar da fashi da makami da sace mutane.

“Kamun na su ya biyo bayan musayar wutan da suka yi ne da dakarun namu, inda a karshe dakarunmu suka damke mutane 23 daga cikin su, sauran kuma suka tsere,” in ji shi.

Kwamnadan ya ce, biyu daga cikin wadanda muka kaman sun sami raunuka na harbi, daya kuma daga cikin sabbin shigan ya mutu sabili da raunukan da ya samu lokacin da ake azabtar da shi wajen shiga kungiyar.

“Sai dai kuma, mu ma daya daga cikin Sojojinmu ya sami raunin harbi da bindiga a kafar shi ta hagu a lokacin musayar wutan, wanda tuni muka wuce da shi asibiti.

Sojan da matsafan biyu duk suna asibitin mu suna karban magani.

“Cikin kayan da muka kama tare da ‘yan kungiyar ta asiri sun hada da wata karamar bindiga mai ta shi biyu ta gida, kwanson harsasai masu rai biyar, adduna biyar, wukake hudu, addunan gida guda uku, da kuma wayoyin hannu guda biyar.

“Mun kuma samu wani kunshin da ake kyautata zaton na tabar Wiwi ce, da katunan ciran kudi na Banki biyu, katunan shaida takwas, kananan hotuna guda takwas, jakunkunan Kwandom da kuma layu kala-kala.

Kwamandan ya kuma ce rundunar na shi ta kai samame wani wajen da ake kyautata zaton na masu lalata bututun mai ne a sassan Ilara da Imagbon na Ikorodu, domin su hana su lalata bututun na mai.

Masu lalata bututun na mai wadanda suke dauke da bindigar AK-47 sun yi ta harbi kafin suka gudu da suka hango jami’an rundunar namu.

“Kayan da muka kwato a tare da su sun hada da, wani kwale-kwalen katako daya, jarkokin mai 40 da kuma bututun janyo mai mai tsawon Mita 100 wanda suke amfani da shi wajen satan man.

“Mun lalata kayan da muka samu a tare da su, duk da ba mu iya kama kowa ba a lokacin,” in ji Udoh.

Kwamandan ya ce, rundunar kuma ta kama mutane bakwai masu yin shigan burtu, tare da masu lalata bututun mai a ranar 17 ga watan Afrilu a Legas da Jihar Ogun.

“A kuma kewayen da muke yi, mun gano wasu wuraren na masu satar man inda muka kama mutane takwas daga cikin masu satan man.

“Kayan da muka samu a wajen su sun hada da, Motoci 10, jarkokin zuba mai 31 dauke da man na Fetur, da kuma wasu jarkokin 77 da ba a kai ga zuba masu man ba, manyan kuloli uku, wayoyin hannu guda tara gami da wasu muggan kwayoyi.

“Mun kuma kama wasu jarkokin guda 1,320, mun kuma kona su.

“Sannan mun kama mutane bakwai a tare da su.

Udoh, ya nu na jin dadin shi bisa hadin kai da goyon bayan da al’ummar na Jihohin Legas da Ogun ke ba su.

“A yanzun haka muna ta kara yin binciken farko kan mutanan da muka kama, bayan nan za mu danka su ga hukumomin da suka dace domin ci gaba da bincike da kuma fuskantar hukunci.”

Makarantar Nurul Hidaya Ta Gudanar Da Bikin Saukar Karatun Dalibai 44

Makarantar Nurul Hidaya Islamiyya Kwasangwami dake Karamar Hukumar Gezawa ta gudanar da bikin saukar Karatun Alkur’ani na Dalibai 44 hudu, ashirin da uku maza da kuma mata 21 karo na uku. Da yake gabatar da jawabin maraba wakilin shugabar sashin ilimi na Karamar Hukumar Gezawa ya bayyana farin cikinsu bisa amsa gayyatar da jam’a da suka yi, saboda haka sai ya bukaci jama’a da suka mai da hankali wajen tarbiyar yara tare da bayar da dukkan hadin kan da malamai ke bukata wajen gudanar da harkokin koyarwa.

Shugaban Makarantar Nurul Hidaya Malam Adamu Abdullahi ana sa jawabin ya fara bayyana kadan daga cikin Tarihin Makarantar wadda yace an kafa Makarantar A shekara 2008 da dalibai 18 da  malami guda daya, amma cikin jinkan Allah yau gashi makarantar na da Daliban da suka haura 1,118, ya ce shekara 2010 ne Makarantar ta samu rijista da hukumar ilimi ta karamar hukumar Gezawa kuma aka turo malamin hukuma guda daya domin ci gaba da bayar da ilimi.

Malam Adamu Abdullahi ya ci gaba da cewa yau kuma alhamdulillahi gashi ana gudanar da bikin saukar Karatun Dalibai 44 maza da mata, wannan ya tabbatar da gagarumar nasarar da ake fata tun lokacin kafuwar wannan Makaranta. Shugaban ya kuma jinjinawa Mai girma Hakimin Gezawa Mai Unguwar Mundubawa Alhaji Muhammadu Yusufu bisa kyakkyawar kulawar da yake baiwa harkokin da suka shafi addini. Haka kuma a lokacin bikin saukar karatun shugaban makarantar ya yiwa Jama’a tanbihin gudumawar da wakilin al’ummar Gabasawa da Gezawa a Majalisar wakilai ta tarayya Honarabul Musa Ado Tsamiya Babba bisa samar da rijiyar burtsatse tare da yiwa Malamai da dalibai kyaututtuka iri daban daban.

Da yake gabatar da nasa Jawabin Hakimin Gezawa Mai unguwar Mundubawa Alhaji Muhammadu Yusufu ya bayyana farin cikinsa bisa ganin yadda wadannan dalibai suka yi dacen sauke alkur’ani, yace garin Gezawa garin Malamai ne saboda haka duk wani al’amarin alkur’ani bana  mamaki idan an  same shi yankin Gezawa, saboda haka sai ya yi addu’a tare da taya murna ga wadannan dalibai da Allah ya horewa samun saukar alkur’ani, daga nan sai ya  hori jama’a da su kara kaimi wajen tabbatar da zaman lafiya da kuma yin kyakkyawan tunani aduk wani al’amarin rayuwa.

Alhaji Aminu Dan Jummai Kwasargwami wanda ya wakilci Honarabul Musa Ado Tsamiya Babba ya bayyana cewa ko shakka babu wannan makaranta tana cikin kahon zuciyar Dan Majalisar Wakilan mai wakilta al’ummar Gabasawa da Gezawa, domin kamar yadda aka sani wannan itace sauka karo na uku wanda kuma kowacce sauka da shi ake, wannan ma wani aikin kasa ne ya tsare shi, saboda haka ya umarce ni da cewar lallai na tabbatar da ganin mun halarci wannan saukar alkur’ani, kuma kamar yadda kowa ya ji aikinsa kadai ake iya gani a wannan makaranta, saboda haka muna tabbatarwa da jama’a cewar da yardar Allah zamu isar da dukkan sakon da ake fatan isarwa Alhaji Musa Ado Tsamiya Babba.

Shugaban gidauniyar Ganduje Alhaji Rabiu Jafar alokacin da yake taya wadannan dalibai murnar sauke alkur’ani bisa, sannan kuma ya gabatar da gudunmawar alkur’anai guda 44 domin rabawa daliban da suka sauke alkur’anin, haka kuma shugaban gidauniyar Ganduje ya tabbatwa da jama’a aniyar Gwamnatin Ganduje na ci gaba da kwararo ayyukan alhairi ga Kanawa.

 

Exit mobile version