Rundunar Sojin Nijeriya ta kama ‘yan ta’adda 25, ta kuma ceto mutane 16 da aka sace, tare da kashe wasu a cikin jerin hare-haren da ta kai a sassan ƙasar nan kwanan nan.
A jihohin Borno da Adamawa, sojoji sun kai wa ‘yan ta’addan ISWAP/JAS a Konduga da Madagali farmaki, inda suka kama wani da ake zargin yana kai musu mai, sannan suka kama man fetur da takin zamani da ake safararsu.
- Sin Da Amurka Na Da Damar Cimma Karin Nasarori Tare Muddin Sun Nacewa Alkawuran Da Suke Dauka
- Saliba Ya Sabunta Kwantiraginsa Da Arsenal Har Tsawon Shekaru 5
Haka kuma an cafke wani da ya kai wasu hare-hare a baya a Garkida.
A Zamfara, sojoji sun daƙile kai hare-hare, sun ceto mutane shida, sun kuma ƙwato babura.
A Kaduna kuma, an kama wani babban mai garkuwa da mutane a ƙaramar hukumar Sanga.
A Benuwe, sojoji sun kashe wani, sun kuma ceto fasinjoji 10 da aka yi garkuwa da su, yayin da aka ceto wasu uku a Kwara.
A Nasarawa, an kama mutane biyu da ke safarar miyagun ƙwayoyi, a Imo kuma, an cafke masu safarar bindigu.
Hakazalika, a Anambra, sojoji sun daƙile ayyukan IPOB/ESN tare da ƙwato abubuwan fashewa.
A jihohin Delta da Bayelsa kuma, an ƙwato bindigogi, harsasai da miyagun ƙwayoyi da yawa.
Sama da lita 1,200 na man fetur da aka tace ba bisa ƙa’ida ba, ak kama a Ribas da Bayelsa.
Gaba ɗaya, sojojin sun ƙwato bindigogi, harsasai, abubuwan fashewa, babura, man fetur, takin zamani da miyagun ƙwayoyi daga hannun ‘yan ta’adda da sauran masu laifi.