Shugaban ma’aikatan shalkwatar tsaron Nijeriya, Manjo Janar Lucky Irabor, ya karyata labarin da ke nuna cewa wai an ceto wasu yan matan Chibok a samamen da sojoji su ka gudanar a arewa maso gabas.
Mista Irabor ya musanta wannan ikirari a tattaunawar da ya yi da manema labarai a ziyarar da ya kai a cibiyar yaki da Boko Haram ta Lafiya Dole da ke birnin Maidugurin jihar Borno ranar Lahadi.
Ya kara da cewa, babu wasu yan matan Chibok da ake ajiye dasu a nan Barikin sojoji.
“Ba mu da wasu yan matan Chibok da su ke a hannun mu, saboda haka kuma, idan har ba sa tare damu a nan, ka ga kuwa babu ta yadda za mu tabbatar da wannan zancen.”
Har wala yau, ya ce, “Duk da wannan shi ne babban burin sojoji na ganin yan matan Chibok sun dawo gida lafiya, sannan kuma idan aikin da muke na samar da tsaro zai taimaka wajen kubutar su, a tunanina mun taka rawar gani.” Ta bakin Irabor.