Umar A Hunkuyi" />

Sojoji Sun Karyata Zargin Bidiyon Hari Da A Ka Kai A Hanyar Numan-Jalingo

Rundunar Sojin kasar nan ta musanta wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sadarwa na yanar gizo, wanda ke nuna wani hari da aka kai a kan hanyar Numan zuwa Jalingo, a Jihar Adamawa da Taraba, rundunar ta ce, sam wannan faifan bidiyon ba gaskiya ne ba.

“Ba wani hari ko kisa da wani ko wasu suka kai kamar yanda ake zargi,” in ji shi.

Mukaddashin daraktan hulda da jama’a na rundunar, Kanar Sagir Musa, ya bayyana cewa, sunan gidan yarin da aka rubuta da Farsanci ne, sannan kuma wajen ma bai yi kama da wurin da ake son a bayyana cewa abin ya auku ba.

“A bisa wannan dalilin, akwai hujjar tabbatar da wannan faifan bidiyon ma ba a cikin kasar nan ne aka dauke shi ba, akwai alamun an kirkire shi ne a daya daga cikin kasashe makwabtanmu masu magana da harshen farasanci, don haka ya kamata al’umma su yi watsi da shi,” in ji shi.

Ya kuma tabbatar da cewa, an sanya jami’an Soja dare da rana a kan hanyar da nufin magance matsalar ‘yan fashi, fadan manoma da makiyaya, masu satar shanu da fadace-fadacen kabilanci da sauran ayyukan laifi.

“Ya kuma tabbata, kasancewar Sojojin da suke kai-komo a kan hanyar, duk wasu fadace-fadace da rigingimu sun ragu sosai a yankunan da sauran sassan da ke da hatsari a Jihohin biyu.”

Ya ce, Jami’an Sojin da aka tura wajen sun san abin da ake son su da aikatawa, a shirye kuma suke da su yi aikin na su na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa nagari a duk wuraren da aka tura su.

Exit mobile version