Idris Aliyu Daudawa" />

Sojoji Sun Kashe Membobin Kungiyar ’Yan Bindiga Ta ‘Gana’ a Binuwai

Sojoji  na rundunar WHIRL STROKE (OPWS) na rundunar sojojin Nijeriya daren jiya suka kashe tawagar ‘yan ta’adda guda ukku wadanda kuma sun e shugabannin kungiyar shugaban wanda ake ta neman shin ruwa a jallo, a jihar Binuwai shugabansu Terwase Akwazaî

Manjo janar Adeyemi Yekini shine wanda ya bayyana hakan a hedikwatar Tactical Air Command dake Makurdi, wadda ta kasance hedikwata ce ta kai hare haren, ya bayyana cewar, su mutanen guda uku anÜkashe su ne lokacin da aka yi musanyar wuta, dasu sojojin a garin Zaki Biam cikin karamar hukumar Ukum ta jihar Binuwai.

Ana iya tunawa dai Janar Yekini a cikin kwana biyu da suka wuce ya bayyanawa manema labarai a Makurdi cewar,n sojojin OPWS sun kashe matar shugaban ‘yan ta’addar Terwase Agwaza, wanda aka fi sanin shi da sunan”Gana” da kuma wasu mambobin shi su goma sha biyu, a Sai karamar hukumar Katsina/Ala, lokacin da suka yi musayar wuta, tsakanin su mambobin da kuma su wadanda ake zargin ‘yan ta’adda ne, dasu da dakarun yakijn “Operation Whirt Stroke OPWS.

Ya bayyana cewar siu dakarun sojojin a Zaki Biam da dare (Lahadin din makon daya gabata) suka samu wani sako wandab yake nuna cewar garin Zaki Biam yana fama da annobar mahara, wadanda suke karkashin Gana, sai kuma su dakarun sojojin suka mayara da martini,wanda kuma da hakan ne aka samu kashe su mambobin guda uku a wurin da aka yi  artabun.

‘’Sojoji wadanda suke da zama kusa da karamar humumar Ukum sun sami sakon cewar Gana shi da mutanen shi, sun shiga cikin garin Zaki Biam suka tsare wasu sassan garin suka fara kashewa da kuma lalata kayayyakin mutane.

“Mutanen mu sun fara kai hari ba tare da bata lokaci ba, ana cikin wannnan yanayin ne kuma suka samu damar kashe, manyan kungiya su uku, ta hanyar musanyar wuta, hakanan ma an samu muggan makamai da kuma albarusai.

 

Exit mobile version