Connect with us

LABARAI

Sojoji Sun Kashe ‘Yan Boko Haram 3 Tare Da Kwato Makamai A Borno

Published

on

Rundunar Soji ta kasa ta ce, dakarunta sun kashe wasu ‘yan kungiyar ta’addan Boko Haram su uku, a wani zagaye da jami’an rundunar suka kai a garin Kukawa, ta karamar hukumar Baga, a Jihar Borno ranar Lahadi.
Daraktan hulda da fararen hula na rundunar, Birgediya Janar Tedas Chukwu ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a Maiduguri ranar Litinin.
Chukwu ya ce, a lokacin da Sojojin ne suke farautar ‘yan Boko Haram din suka sami labarin su a kauyan Kalamari, mai tazarar kilomita 30 daga garin na Kukawa.
Ya ce, a daidai lokacin da ‘yan ta’addan suke ta kwashe wa mazauna kauyan kadarorin su ne Sojojin daga rundunar Sojin ta, ‘Operation Lafiya Dole,’ suka diran masu.
“A sa’ilin da suka fafata ne Sojojin suka sha karfin ‘yan ta’addan inda har suka kashe uku daga cikin su.
Daraktan ya ce, sun kuma kwato bindigogin AK47 guda uku, kwanson harsasai biyu da kuma curi hudu na harsashin 7.62mm, daga hannun su.
“A yanzun haka zaratan Sojojin namu sun bi bayan sauran ‘yan kungiyar ‘yan ta’addan ta Boko Haram da suka ranta a na kare zuwa maboyar su da nufin su kamo su.
“Ana shawartan al’umma da su kai rahoton duk wani take-taken da ba su fahimta ba ga hukumomin da suka dace domin daukan mataki a cikin gaggawa.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: