Sulaiman Ibrahim" />

Sojoji Sun Kashe ‘Yan Boko Haram Da Yawa A Damboa Ta Jihar Borno

Dakarun rundunar’ Operation Fire Ball’ a karkashin rundunar ‘Operation LAFIYA DOLE’ na ci gaba da fatattakar mambobin kungiyar Boko Haram / Islamic State of West domin karkade ragowar ‘yan ta’addan daga yankin.

Wasu daga cikin bindigogin da aka kwato

A irin wannan nasarar ce, a ranar 25 ga Oktoba 2020 wani Abu ya faru da ‘yan boko Haram Wanda wannan za a iya kamanta shi da kunar bakin wake da kungiyar tayi, yayin da ta kai hari a kan Sojoji da ke sansanin soja na Super Camp Damboa a karkashin rundunar 25 Bde yanki na 2.
‘Yan ta’addar sun hadu da fushin rundunar yayin da ta doke su tare da yi musu ruwan harsashi da karin gobarar wuta daga Rundunar Sojan Sama.
Rundunar boko Haram dole suka ja baya don baza su iya ja da sojoji kwararru Masu tsari yayin artabu ba. ‘Yan ta’addan na Boko Haram sun tsira da munanan raunuka na Harbin bindiga yayin da 22 suka rasa rayukansu, an kuma samu nasarar lalata manyan motocin Bindigogi 2, an kwato Bindigar Jirgin Sama na NSV guda daya, 2 Rockect Propelled Grenade Tubes, 4 PKT Machine Gun, General Purpose Machine Gun, Bindigar da ake hadawa da Browning 1, da Rifle 12Ak 47, da bindiga AK 74. Sauran kayayyakin sun hada da: Bom 1, RPG 7, Round 116 na 7.62mm NATO da gurnetin hannu 2.

Kadan ne daga cikin sojojinmu suka ji rauni a wajen kuma yanzu haka ankwashe su zuwa wajen amsar magani.

An yabawa sojojin ‘Operation Fire Ball’ karkashin rundunar ‘Operation LAFIYA DOLE’ saboda juriya da jajircewarsu da suka nuna tun farkon kaddamar da rundunar ta ‘ Operation fire Ball’. An kuma yaba da hazakarsu da jajircewarsu inda aka nemesu da cewa kar su huta su cigaba da kafa nasara kan nasarorin da suka kafa.

Rundunar ta tabbatar wa daukacin al’ummar yankin Arewa maso Gabas ce wa, rundunar sojin Nijeriya zata cigaba da jajircewa domin ganin ta fatattaki ragowar mayakan BHT / ISWAP daga yankin.

BENARD ONYEUKO
Birgediya Janar
Ag Darakta
Ayyukan Media na Tsaro
29 Oktoba 2020

Exit mobile version