Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda Da Dama A Yankin Tafkin Chadi

Ibo

Daga Bello Hamza,

Dakarun Sojojin Nijeriya na ‘Operation Lafiya Dole’ sun samu nasarar kashe ‘yan ta’addan Boko Haram da na ‘yan ISWAP da dama a jihar Borno a wani fattaka da suka kai musu ranar Asabar.

Jami’in watsa labarai na rundunar, Brig.-Gen. Mohammed Yerima, ya bayyana haka a sanarwa da ya raba wa manema labarai a garin Abuja ranar Litinin.

Janar Yerima ya kuma kara bayyana cewa, an yi artabun ne a yankin tafkin tekun Chadi an kuma samu nasarar lalata motoci masu daukar bindiga na ‘yan ta’addan an kuma samu kwace bindigogi da albarushai da dama daga maboyar ‘yan ta’addan.

Ya ce, dakarun sun yi artabun ne da ‘yan ta’adda a yankin kauyukan Daban Massara da Ali Sherifti in da suka samu nasarar fattakar ‘yan ta’addan gaba daya.

Tuni kuma sojoji suka fara zango na biyu na yakin da suke yi da ‘yan ta’addan a bangaren hanyar da ta taso daga Kukawa zuwa Monguno, in da a nisan kilo mita 14 daga sansanin su suka hango motar daukar bindiga na ‘yan ta’adda inda suka fattake su.

“Muna kira ga al’umma su cigaba da bamu goyon baya don ganin an fatattaki ‘yan ta’addan gaba daya, kamar yadda shugaban rundunar sojin Nijeriya ya umarta,” inji shi.

 

Exit mobile version