Mahdi M Muhammad" />

Sojoji Sun Katse Bayar Da Kudin Fansa Ga Boko Haram

Kudin Fansa

Sojojin Nijeriya sun samu nasarar kawo cikas wajen biyan kudin fansa daga wasu da ake zargin Boko Haram ta yi garkuwa da su.

A wata sanarwa da mukaddashin Daraktan yada labarai na tsaro, Birgediya Janar, Benard Onyeuko ya fitar a ranar 17 ga Nuwamba, 2020, ya bayyana cewa, rundunar Bataliya ta 151 da aka a jiye a yankin da ake kira ‘Strong Response Area (SRA)’ Molai, don yin aiki da sahihan bayanan sirri, sun cafke wasu ’ya’yan Boko Haram da wasu mutanen da aka sace a daidai lokacin da suke kokarin biyan kudin fansar Naira Miliyan 2 ga ‘yan ta’addan.

Sanarwar ta kara da cewa, “a cikin hanzarin kai dauki, sojojin sun kai hari don yin artabu da ‘yan Boko Haram din, tare da tilasta dakatar da karbar kudaden fansar, da kuma sanya su sakin wadanda suka sace.

“Daya daga cikin ‘yan ta’addan Boko Haram din an kashe shi, yayin da wasu daga cikin su suka tsere da munanan raunukan harbin bindiga. An gano bindiga mai kirar AK 47 da babur a wurin faruwar lamarin. Wadanda lamarin ya rutsa da su, ciki har da mata biyu da yara kanana, kuma duk an samu damar kubutar da su ba tare da ko kwarzane ba,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “a wani ci gaban kuma, a ranar 17 ga Nuwamba, 2020, sojoji na Bataliya 151 sun gudanar da sintiri na yaki don share maboyar ‘yan Boko Haram a kauyen Zaye Ngusa. Dakarun ‘eagle-eayed’ sun hango masu laifin kuma sun shige su tare da karfin wuta wanda ya tilasta su ficewa cikin rudani yayin da jini ke kwarara a hanyoyinsu na tserewa. Daya daga cikin ‘yan ta’addar an kashe shi.”

“A wannan ranar ne kuma sojojin bataliya ta 202 suka yi nasarar yakin kwantar bauna a inda suka bi daya daga cikin masu laifin wanda ya kai ga zuwa inda sauran suke, a yayin hakan ne bataliyan suka samu damar kawar da wani babban mai laifi na Boko Haram din, yayin da wasu da dama ake jin sun tsere da munanan raunuka daban-daban na harbin bindiga a karkashin duhun.”

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “haka zalika, a ranar 15 ga Nuwamba, 2020, sojojin ’26 Task Force Brigade SRA Pulka’ sun samu kyakkyawar nasarar kwanton bauna a kan hanyar Pulka-Sabon Gari-Kirawa, a inda tare ayarin motocin Boko Haram. Lokacin da sojojin suka ga ‘yan ta’addan din, sai suka fara musayar wuta da su wanda hakan ya tilasta su gudu da kuma yin watsi da kayansu. Kayayyakin da aka kwato daga wurin su sun hada da kekuna takwas, buhunan hatsi da yawa, buhuhunan magunguna da sauran kayan abinci.”

Exit mobile version