Kwamandan runduna ta 13 ta sojojin Nijeriya, Birgediya Janar Mohammed A. Abdullahi, ya mika wasu mutane hudu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne ga rundunar ‘yan sandan Nijeriya a kalaba.
Abdullahi ya gabatar da wadanda ake zargin ne a hedikwatar rundunar da ke Kalaba a ranar Litinin, inda Manjo Stanley N. Ikpeme wanda ya wakilce shi, ya ce, binciken ya biyo bayan bin diddigin mutum takwas ne da ake zargi.
Ikpeme ya bayyana cewa, wadanda ake zargin sun yiwa Mista Akan Udoh fashin kudi har Naira 25,000.
Wanda ake zargi na hudu da aka mika wa ‘yan sanda, Peter Obri, an cafke shi da karamar bindiga a gonar dabino a Biase, yayin da wanda yake tare da shi, Bassey har yanzu ba a gano shi ba.
“Mutum na uku da ake zargi, Micah Edet, Bassey Udoh da Emmanuel Bassey, mambobin NSCDC da ke aiki da OP Akpakwu ne suka kama su a ranar 8 ga Fabrairu, 2021, saboda yi wa Mista Akan fashin rana ta Naira 25,000. A lokacin bincike, an gano cewa akwai wani mahallin da wadanda ake zargin suka mayar wurin boyarsu, inda suke kwana da dare,” in ji shi.
Ya ci gaba da cewa, “Haka zalika, Peter Obri, mai shekaru 25, an kame shi a ranar 13 ga Janairun 2021 a gonar Ibiae Rubber tare da karamar bindigar ta kirar gida a yayin da yake kokarin satar ‘ya’yan itacen dabino.”
Ya ce, an mika wadanda ake zargin ga rundunar ‘yan sanda ta Jihar Kuros Riba don ci gaba da bincike tare da hukunta su.
A cikin ikirarinsu, daya daga cikin wadanda ake zargin, Peter Obri, ya ce bai san cewa za su je gonar don yin fashin ba ne, kuma ya kasance tare da abokansa ne kawai.
“Wani abokina ya ce, na raka shi ya dauki wani abu, wnada zai zama banga ne, inda ya ajiye kuma a kan hanyarmu ya ba ni wannan karamar bindiga kirar gida. Na tambaye shi abin da yake son amfani da shi sai ya ce kawai ya rike min. Lokacin da muka isa wurin, ba mu ga banga ba, kuma abin da ba mu sani ba sojoji sun yi mana kwanton bauna, kuma sun kama ni yayin da abokina ya tsere. Ni dan acaba ne, kuma ban san dalilin da ya sa ya nemi in rike masa bindiga ba,” in ji shi.