Daga Sulaiman Ibrahim
Sojojin Nijeriya a yammacin yau, da misalin karfe 3 na yamma, sun kwato garin Marte da sauran al’ummomin da ke kusa da garin daga ‘yan ta’addan Boko Haram.
Wannan na zuwa ne kasa da umarnin awanni 48 da shugaban rundunar sojin kasa, Manjo Janar Ibrahim Attahiru ya baiwa sojojin tun farko.
Sojojin sun samu karin karfin gwiwa daga rundunar sojojin sama na kasa, inda suka samu nasarar afkawa cikin garin Marte, bayan samun nasarar lalata bama-bamai(IEDs) da nakiyoyi da aka binne a kan hanyoyin su, rundunar ta kara samun nasarar kashe ‘yan ta’addan Boko Haram / ISWAP da dama kuma sun samu nasarar kwato garin.