Dakarun runduna ta 6 sashe ta 3 a karkashin rundunar ‘Operation Whirl Stroke (OPWS)’ na rundunar sojojin Nijeriya sun tarwatsa maɓoyar ‘yan bindiga 11 a wasu kananan hukumomi biyu na jihar Taraba.
Mukaddashin Daraktan hulda da jama’a na rundunar soji ta 6, Laftanar Umar Muhammad, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Jalingo, ya bayyana sansanonin ‘yan bindigar da sojojin suka kai wa hari da suka hada da na Tarhembe, Tornyi, da Kando a Tati, karamar hukumar Takum ta jihar.
Laftanar Muhammad ya ce daya daga cikin maɓoyar da aka tarwatsa tana kusa da gonar TY da ke karamar hukumar Takum, kamar yadda aka ce ‘yan bindigar sun lalata gonaki a karamar hukumar Ussa.
Sanarwar ta ce, hare-haren kakkaɓe maɓoyar ‘yan bindigar na zuwa ne a karkashin shirin ‘Operation Lafiya Nakowa’, da nufin fatattakar ‘yan bindiga da sauran masu aikata laifuka a jihar Taraba.
Ya kara da cewa, harin ya biyo bayan sahihan bayanan sirri kan ayyukan ‘yan ta’addan a kusa da Tarhembe, Tornyi, TY Farm, da ɗaukacin yankin Kando da ke yankin Tati, karamar hukumar Takum, da kuma rahotannin lalata gonaki a karamar hukumar Ussa.