Rundunar sojan Najeriya ta bayyana samun nasarar tarwatsa sansanin da mayakan Boko Haram ke amfani dashi wajen horas da mayakansu hadi da lalata rumbun makaman da kungiyar a jihar Borno.
Bayanin hakan ya na kunshe ne a sanrawar manema labarai mai dauke da sa hannun Daraktan yada labaran sojan Nijeriya, Manjo Janar John Eneche, ranar Asabar, inda ya kara da cewa dakarun Lafiya Dole sun samu wannan nasarar ce a farmakin da su ka kaddamar a yankin Nuwar da ke karamar hukumar Bama a jihar Borno, inda su ka kashe mayakan Boko Haram da dama, ranar 14 ga Janairun 2021.
Rundunar sojojin ta sanar da hakan a daidai lokacin da wasu rahotanni ke nuni da cewa bangaren Boko Haram wanda ake kira ISWAP, sun mamaye sansanin sojojin Nijeriya da ke garin Marte, bayan zazzafar fafatawa da ya gudana cikin daren ranar Jummu’a, wayewar ranar Asabar.
Bugu da kari kuma, wasu majiyoyi a yankin sun bayyana cewa Boko Haram sun yi wa dakarun sojojin Nijeriya barna a farnakin na garin Marte, wanda a hannu guda kuma rundunar sojojin ta bayyana cewa ta yi amfani da kwarewa ne wajen janye dakarun ta, yayin da daga bisani ta sanar da sake kwace sansanin sojojin da aka mamayen.