Sojoji Sun ‘Yanto Mutum 4 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Kaduna

Rundunar atisayen Thunder Strike ta Sojoin Nijeriya sun ‘yanto wadansu dalibai hudu na makarantar Sakandaren gwamnati dake Gwagwada a karamar hukumar Chikun na jihar Kaduna wadanda aka sace a hanyarsu ta zuwa makaranta a ranar 10 ga watan Oktoba.

Mataimakin Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na Runduna ta 1 dake Kaduna, Kanal Ezindu Idimah shi ne ya shaidawa manema labarai hakan a daren ranar Litinin. Inda ya tabbatar da cewa; tuni aka mika daliban ya zuwa ga iyayensu dake kauyen Gurmi.

A ranar 10 ga watan Oktoba ne, ‘yan bindigar da suka addabi hanyar Kaduna zuwa Abuja sace daliban makarantar guda 10. Inda bayan agajin da rundunar sojin ta kai, ta yi nasarar ‘yanto shida cikin 10. Inda ‘yan bindigar suka gudu da sauran hudun cikin daji. Inda kuma a ranar Litinin da misalin karfe shida na safe, bayan samun labarin sirri, rundunar sojin ta ‘yanto sauran daliban hudun a maboyar ‘yan bindigar.

 

Exit mobile version