Rahotanni daga Ouagadougou babban birnin kasar Burkina Faso suna alamta yanzu haka sojojin da ke adawa da gwamnatin farar hula suna tsare da Shugaba Roch Marc Christian Kabore da wasu ministocinsa a wani sansaninsu da ke babban birnin kasar.
A wani sakon Twitter da aka wallafa, shugaban Burkina Faso Roch Kabore, ya yi kira ga sojojin da ke mishi bore da su gaggauta ajiye makamansu don mutunta tsarin dimukaradiyya da aka dora kasar a kai.
Sai dai babu wanda ya san halin da yake ciki zuwa yanzu. Shi dai Kabore bai bayyana a bainar jama’a ba tun bayan da sojojin kasarsa suka fara bore. Amma majiyoyi sun shaida cewa yana hannu tare da mukarrabansa a wani barikin soji da ke a birnin Ouagadougou, kazalika sojojin sun karbe iko da gidan talabiji na gwamnati, wanda hakan ke nuna alamun juyin mulkin ne.