Sojojin Kasar Sin Sun Harba Sabon Nau’in Makami Mai Linzami

Daga CRI Hausa,

Kwanan nan ne, sojojin harba makamai masu linzami na rundunar sojan ‘yantar da al’ummar kasar Sin suka harba sabon nau’in wasu makamai masu linzami guda biyu, wadanda suka yi nasarar kaiwa inda aka nufa mai tazarar kilomita sama da dari.

Nasarar da sojojin kasar ta Sin suka samu a wannan karo, ta sa an fadada nau’ikan kawunan makamai masu linzami da ake amfani da su, da kyautata ingancin makaman da za su iya kaiwa inda aka nufa, da maganin illolin da aka yi musu, da kuma kara kwarewarsu na kai hari kan abokan gaba. (Murtala Zhang)

Exit mobile version