Rundunar sojin Mali tace dakarunta sun yi nasarar halaka ‘yan ta’adda akalla 12, a lokacin da suka kaiwa jami’an sojin nata farmaki lokacin da suke sintiri akan iyakar kasar da Burkina Faso.
Cikin sanarwar da ta wallafa a shafinta na Twitter, rundunar sojin Malin tace sun fafata da ‘yan ta’addan ne a ranar Alhamis da ta gabata, kuma babu jami’in da ta rasa yayin gumurzun.
Tun shekarar 2012 Mali ke fama da hare-haren ta’addanci da aka soma fuskanta a arewacin kasar, daga bisani kuma ya bazu zuwa yankin tsakiyar kasar mai fama da rikicin kabilanci a gefe guda.