Connect with us

LABARAI

Sojojin Nijeriya Sun Kashe ’Yan Boko Haram 14 A Borno

Published

on

Sojojin da ke aikin share guggubin ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram, sun sami nasarar ceto wasu da ‘yan ta’addan suka yi garkuwa da su 146, a tsakankanin ranakun Lahadi da Litinin a karamar hukumar Gwoza, ta Jihar Borno.

Cikin sanarwar da daraktan hulda da fararen hula na rundunar, Tedas Chukwu ya fitar ya ce, Sojojin kuma sun kashe ‘yan ta’addan 14, Sun kuma kwato wasu dabbobi daga hannun ‘yan ta’addan.

Daraktan ya ce, a yanzun haka suna tantance mutanan da suka ceto kafin su hannanta su ga hukumomin da suka dace.

Sai dai daraktan ya ce, akwai jami’in Soja guda da ya sami rauni a sakamakon fafatawar wanda a yanzun haka yake karban magani a asibitin na Soji.

A wani abu kuma mai kama da wannan, Mista Chukwu, ya ce dakarun da ke fafatawa a sashe na 3 na rundunar ta, ‘Operation Lafiya Dole,’ da aka tura su kauyan, Keken da ke karamar hukumar Kukawa, ta Jihar Borno, sun dakile wani harin da ‘yan

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: