Sojojin Nijeriya Sun Tarwatsa Gungun Boko Haram A Goniri Ta Borno

Sojojin Nijeriya da suke a Goniri, ta karamar hukumar Gujba, a Jihar Yobe, sun fatattaki wani harin da ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram suka kai masu a ranar Alhamis.

A ranar Litinin ‘yan ta’addan sun murkushe wata cibiyar Sojoji da ke Kukareta, wani kauye da ke da nisan kilomita 20 daga garin Damaturu, Jihar Yobe, inda suka kashe Sojoji 13 da Jami’in ‘yan sanda guda.

“Ana ta bukukuwan murna a garin na Goniri a yanzun haka, ba daya daga cikin ‘yan ta’addan da ya tsira. Duk an kashe su, gawarwakin su ne nan birjik ko-ta-ina, ba dayan su da ya tsira, in ji wata majiyar Soji.

A wani rahoton mai kama da wannan kuma, rundunar Sojin sama ta bayar da bayanan yanda ta taimakawa rundunar mayakan, Operation LAFIYA DOLE, da abokanan aikinta wajen murkushe farmakin da ‘yan ta’addan na Boko Haram suka kai a garin Baga.

Daraktan hulda da fararen hula na rundunar Sojin saman, Aeya Kwamando Ibikunle Daramola, ne ya bayar da bayanin, inda ya shaida cewa rundunar Sojin saman ta kai hare-hare sama da dozin guda a kan ‘yan ta’addan.

Bayanin na cewa, “In za a tuna, Shalkwatar bataliyan hadin gwiwa ta (MNJTF) da ke Baga, ta sami farmaki daga ‘yan kungiyar ta’addanci na kasar Musulunci a yankin yammacin Afrika, (ISWAP) a yammacin ranar 26 ga watan Disamba.

“Da samun labarin farmakin, sai rundunarmu ta sojin sama (ATF) da ke aiki da rundunar, Operation LAFIYA DOLE, ta hanzarta aikewa da Jirage masu binciken sirra da kuma wasu Jiragen Helikwafta biyu masu aman wuta domin su tallafawa dakarun Sojin na kasa murkushe farmakin.

“Dakarun namu da ke sama suna yin magana da dakarun na kasa, wadanda suka taimaka masu wajen nuna masu daidai wajen da ‘yan ta’addan suke inda suka yi ta masu aman wuta, Jiragen saman na Helikwafta kuma suka yi ta farma ‘yan ta’addan da harbi a wani wuri na daban da aka iya taskace su, har suka lalata wasu daga cikin motocin su suka kuma kashe da yawa daga cikin mayakan na su,” in ji shi.

“Bayan samun tabbacin inda ‘yan ta’addan suke ne ta bayanan da dakarun kasan suke ba mu, sai Jiragen yakin mu samfurin Alpha Jet, suka yi ta kai masu farmaki.

Kakakin rundunar ya ce, gabaki-daya, rundunar na su ta kai farmaki ne sau 20 da da hari 21 na tsawon awanni 39 a ranakun 26 da 27 ga watan Disamba, domin tallafawa dakarun kasa a garin na Baga, da kewayen sa.

Exit mobile version