Sojojin Nijeriya Sun Yi Gargadi Ga Igboho Da Masu Ikirarin Raba Kasa

Daga Rabiu Ali Indabawa,

Babban Hafsan Hafsoshin Sojan Kasa na Nijeriya, Laftanar Janar Ibrahim Attahiru ya fada a ranar Litinin cewa sojoji sun shirya tsaf don tunkarar masu neman ballewa daga kasar da nufin wargaza Nijeriya kamar su Sunday Igboho da Asari Dokubo.

An bayar da gargadin Attahiru ne a Uyo a taron farko na Ofishin Shugabanni na 2021. Kwanan nan, mai neman jawo rikici a yankin Yarbawa, Sunday Igboho da sauransu a yankin Kudu maso Yamma sun yi ta kausasa kalamai kan cewa yankin Yarbawa ya balle daga Nijeriya.

Igboho ya bayyana cewa yankin Kudu maso Yammacin kasar nan ba ya cikin Nijeriya.

Haka shi ma Dokubo, a nasa bangaren ya kuma sanar da kafa Gwamnatin Al’adun Biafra inda ya sanya wasu bangarorin Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu a matsayin wani yanki daga cikin yankin.

Dangane da ci gaban, Babban Hafsan Hafsoshin Sojan Attahiru, ya ba da tabbacin cewa Sojojin Nijeriya za su yi maganin duk wata barazanar tsaro da ke tunkarar kasar, ciki har da wadanda ke tayar da zaune tsaye kamar su Igboho da Dokubo suka kawo.

Attahiru ya tabbatarwa da kasar cewa Sojojin Nijeriya nan ba da dadewa ba za su shawo kan yunkurin da wasu mutane ke yi na lalata wasu yankunan kasar ta hanyar ayyana ikon mallaka a madadin kabilun kasar.

“Sojojin Nijeriya a karkashin jagoranci na za su ci gaba da aiki tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro don magance barazanar da kasar ke fuskanta.

“Sojojin Nijeriya da ke karkashina na nan daram kuma sun shirya sosai fiye da kowane lokaci don magance mutane ko kungiyoyin da ke barazana ga zaman lafiya, tsaro da kwanciyar hankali na wannan kasa tamu,” inji shi.

Attahiru ya yi kira ga mahalarta taron bitar da aka yi wa taken, “Sake tura Sojojin Nijeriya don fatattakar masu adawa da zaman lafiya a cikin wani Muhallin hadin gwiwa.” su sadaukar da kansu ga abin da suka wajabta wa al’umma.

COAS din ya ce zai ci gaba da ba da horo kan manufa ta hanyar bita da kuma inganta karfin soji wanda zai sa sojojin su kasance masu dogaro da kuma rashin jin tsoron duk masu adawa.

A nasa jawabin, Gwamna Udom Emmanuel na Akwa Ibom ya ce dangane da kalubalen tsaro da ke addabar al’ummar kasar, ya yi kira da a samar da sojoji wadanda za su kasance a shirye kuma su magance matsalolin don fuskantar ko wace barazana.

Emmanuel, wanda ya samu wakilcin Mataimakin Gwamnan, Mista Moses Ekpo, ya bukaci sojoji su kara kaimi da fadada dabaru, dabarun da ake bukata don dakile duk matsalar rashin tsaro a fadin kasar.

Ya yaba wa hukumomin tsaro da dama a jihar kan hadin kai da aiki tare a tsakaninsu wanda ya ce ya kawo tsaro a jihar, ya kuma yi alkawarin ci gaba da tallafa musu.

“Tare da al’amuran tsaro da ke fuskantar kasarmu, sojoji ya kamata fiye da kowane lokaci su kasance a shirye don fuskantar wadannan abubuwan ta hanyar tabbatar da cewa aikin zai ci gaba da kasancewa mafi girman matsayin ci gaba tare da samun tabbataccen horo.

Emmanuel ya ce “Abin kwantar da hankali ne cewa duk da sauran alkawurran aiki a duk fadin kasar, sabon shugaban hafsan sojojin ya ga ya dace a shirya wannan taron bita,” in ji Emmanuel.

Exit mobile version