Rundunar sojin saman Nijeriya, ta fara gudanar da aikin tallafawa wadanda ambaliyar ruwa ya jikkata a Wauru-Jabbe dake karamar hukumar Yola a jihar Adamawa. Rundunar sun fara tallafawa wadanda ambaliyar ruwan ya shafa ne da bada magunguna.
A yayin da suke gudanar da aikin a ranar Litinin, Air Marshal Saddique Abubakar, ya ce wannan aikin yana daya daga cikin ayyukan jin kai da NAF din ke gudanarwa domin ganin sun tallafawa tare da rage radadin wadanda ambaliyar ya shafa.
Abubakar, wanda Air Cdr Mohammed Yusufu, ya wakilce shi, ya ce wannan aikin na su daya ne daga cikin dimbin aikin da rundunar take yi wajen bunaksa huldar dake tsakanin soji da fararen hula.
Ya ce sun zabi su tallafawa Wauru-Jabbe ne domin su ambaliyar ruwan ya fi jikkatawa.