Sojojin saman Nijeriya a karkashin rundunar yaki da Boko Haram ta Lafiya Dole sun yi nasarar wargaza sabuwar tungar mayakan da ke jihar Borno.
Shalkwatar tsaro ta Nijeriya ce ta sanar da hakan a sanarwar manema labarai mai dauke da sa-hannun jami’in hulda da jama’a, Manjo Janar John Enench a ranar Asabar, inda ya kara da cewa sun samu wannan nasara ne ranar 1 ga Junairun 2021 a garin Mana Waji da ke jihar Borni.
“Sojojin mu na sama a karkashin Lafiya Dole sun gudanar da wannan samamen, ta hanyar yin ruwan bama-bamai a sansanin, a ci gaba da yaki da yan ta’adda a yankin arewa maso gabas, a kokarin kakkabe mayakan Boko Haram da kayayyakin su.”
“Bugu da kari kuma, an aiwatar da harin tarwatsa wannan sabuwar tungar maharan wanda jiragen yaki na sojojin saman Nijeriya (NAF) ta hanyar barin wuta da sauran makamai a inda yan ta’addan suke da makaman su tare da sauran kayayyakin da suka mallaka a wajen wanda su ka kitsa aiwatar da kai munanan hare-hare.”