An sake soke zaman majalisar Ministoci a karo na biyu tun bayan dawowar Shugaba Muhammad Buhari jinya daga birnin Landan.
An dai soke zaman majalisar ministocin ne wanda aka saba gudanarwa a duk ranar Laraba.
A cewar Ministan Yada Labarai na Nijeriya, Lai Mohammed ya ce an soke zaman majalisar ne saboda rashin isasshen lokaci da ministocin za su yi nazari kan batutuwan da aka tsara tattaunawa a lokacin zaman sakamakon hutun bukukuwan Babban sallah da aka gudanar.