Gwamnatin ƙasar Somalia ta ce ta kashe ƙaya daga cikin shugabanin ƙungiyar Al Shebaab Moalim Osman Abdi Badil tare da wasu jami’ansa guda uku a Yankin Shabelle. Wannan na zuwa bayan kisan wani Sojan Amurka.
Ministan yaƙa labaran ƙasar ya ce sojojin Somalia ne suka kai harin da ya hallaka shugaban, kuma wannan ba ƙaramar nasara ba ce a ci gaba da yakin da suke da y’an ta’adda. A ranar juma’ar da ta gabata, ƙungiyar Al Shebaab ta kashe wani sojan Amurka guda tare da raunana wasu biyu. Kasar Somalia ta kasa samun zaman lafiya tun bayan kifar da gwamnatin Shugaba Siad Barre a shekarar 1991.