Daga Khalid Idris Doya, Bauchi
Gwamnatin Jihar Bauchi ta bayyana cewar za ta sanya hannu kan takardar yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) da hukumar tabbatar da ingancin kayayyaki ta Nijeriya (SON) domin tabbatar da ingancin kayayyakin da ake fitarwa daga cikin jihar da kuma wadanda ake shigowa da su.
Gwamnan jihar Bala Muhammad shi ne ya shaida hakan a lokacin da ya amshi bakwancin Babban Daraktan (SON) na kasa, Alhaji Faruk Salim, da ya ziyarce shi a gidan gwamnatin Bauchi.
Gwamnan wanda ya nuna kwarin guiwar cewa ta hanyar yin aikin hadin guiwa da hukumar ta SON za a samu damar baiwa manoman jihar damar fitar da kayayyakin amfanin gona zuwa wasu jihohi da ma kasashen waje da suke nomawa domin ci gaba mai ma’ana.
Bala, ya jaddada aniyar gwamnatinsa na yin hadakan domin alfanun da al’umman jihar za su samu daga aikace-aikacen hukumar na tabbatar da ingancin kayan da ake shigowa da su ko fitarwa daga cikin jihar.
Gwamnan ya ce akwai matasan da basu da ayyukan yi a shiyyar arewa maso gabas wannan ne ya sanya su gwamnoni suka maida hankali wajen mara baya ga dukkanin wata hukumar da za ta bada gudunmawa wa shirye-shiryensu da tsare-tsarensu na dakile matsalar rashin aikin yi a tsakanin jama’a domin rage matsalar talauci da fatara a tsakanin mutane.
Gwamnan ya ce: “A shirye muke a gwamnatance mu sanya hannu kan jarjejeniya da hukumar SON kamar yadda suke sanyawa da sauran jihohi inda za a samu maslaha wajen neman ingancin da inganta abubuwan da suke shigowa kamar maguna da sauran kayayayyakin da ‘yan kasuwa ke shigowa da su, da kuma muma wadanda muke fitarwa.
“Za mu yi amfana da hazaka da ilimin da basiran yaranmu, kun ga yadda yaranmu suke kokari, don ganin muma ana sarrafa kayayyaki a cikin jihar nan don fitar da su waje domin samun cigaba,” inji gwamnan.
Shi kuma a nasa fannin, Darakta Janar na hukumar kula da ingancin kayayyaki ta kasa, Faruk Salim, ya tabbatar da cewar da wannan hadin kai da za su yi, hukumar za ta samu saukin gudanar da ayyukanta a jihar da ma jihohin da suke makwafta da Bauchi.
Salim, ya kuma bayyana cewar dukkanin kayan da hukumarsu ta amince da su domin fitarwa zuwa kasashen waje kaya ne masu inganci da aka tantance, sai dai ya nuna damuwarsa kan wasu bata-gari da ke safaran kayayyaki ba tare da sahalewar hukumar ba wanda ya misalta hakan da cewa sune marasa inganci, “Duk kayan da muke fitarwa daga cikin Nijeriya masu kyau ne.”
Kan masu safaran kayan da babu tantancewar ingancisu, ya ce suna da mutanen da suke bibiya da binciken wadanda suke fitar da kaya marasa kyau, “Sannan muna da na’urorin da muke bi wajen tattace kayayyakin da ake sarrafawa domin tabbatar da jama’a suna amfani da kayayyakin da suka dace masu inganci.”
Shugaban hukumar ya bayyana cewar manyan kalubalen da suke fuskanta a halin yanzu sun hada da mutane masu kunnen kashi da ke bin barauniyar hanya wajen sayo kayayyakin da basu da kyau don shigowa da su cikin kasar nan, “Suna nasu kokarin muma muna namu, muna shiga lunguna da sakona domin kama masu irin wannan kuma muna gurfanar da su a kotu.”
Ya ce, agajin da gwamnatin Bauchi ta ce za ta musu zai taimaka wa kokarin hukumar wajen ganin sun inganta ayyukansu na tsarkake kayan da ake shigowa da su ko ake fita da su domin tabbatar da ana jigila ko safaran ingantattun kayayyaki a cikin jama’a.