SON Za Ta Fara Amfani Da Wata Alamar Tantance Ingantattun Kayayyaki A Nijeriya

Hukumar tabbatar da ingancin kayyaki a Nijeriya wato ‘Standards Organisaton of Nigeria’ ta shirya tsaf domin fitar da wata sabon tsari mai suna ‘PAM’ wacce za ta ke alamarta dukkanin wani kayan da ke da inganci gami da sahalewa daga hukumomin da abun ya shafa a fadin Nijeriya domin kare ‘yan kasa daga amfani da gurbattattun kayyakin amfani.

Hakan na cikin shirin hukumar ne na tabbatar da an tsaftace dukkanin kayyakin da jama’an kasa ke amfani da su, domin shawo kan yawaitar gurbatattun kayyakin amfani yau da kullum a cikin Nijeriya. A wani taron kara wa juna sani kan wannan sabon tsarin da za SON za ta fara amfani da shi wadda aka shirya wa masu ruwa da tsaki na shiyyar Arewa Maso Gabas a Jihar Bauchi ya guda na ne a dakin taro na DEC a Jiya Litinin.

Taron kara wa juna sanin na shiyyar Arewa Maso Gabas ya hada da Masu yin kayyakin, da masu shigo da kayyaki, da kuma masu fitar da kayyaki, hade kuma da masu amfani da kayyakin amfani yau da gobe da suke Nijeriya. mahalartar sun fito ne daga jahohin Bauchi, Adamawa, Gombe, Borno, Yobe da kuma Taraba.

Da yake bayani kan wannan sabon tsarin da za su kaddamar mai suna PAM, shugaban hukumar tabbatar da inganci kayyaki a Nijeriya Mr. Osita Abiloma Anthony ya bayyana cewar wannan shirin nasu zai kawo ci gaba ta fuskacin tabbatar da inganci kayyaki da kuma dakile yawaitar gurbattatun kayyaki da ake shigowar cikin kasuwannin Nijeriya domin amfani

Ta bakinsa shugaban SON na kasa, wadda ya samu wakilcin Alhaji Umar Yakubu, shugaban hukumar a Jihar Gombe ya ce “Muna kokarin fadar da wayar da kan jama’a kan cewar akwai sabon tsarin da muke son mu kaddamar domin tsaftace dukkanin kayyakin amfanin a Nijeriya. za mu kaddamar gami da fara amfani da wannan sabon tsarin ne a ranar Alhamis 1 ga watan Fabrairun 2018 domin ci gaba da shawo kan gurbattatun kayyaki a Nijeriya”. A cewarsa.

Shugaban ya ci gaba da cewa “wannan sabon tsarin mai suna ‘Product Authentication Mark PAM’ zai ke tabbatar da cewar dukkanin kayyakin da jama’an kasa ke amfani da su, suna da ingancin da suka dace a yi amfani da su, kuma mune muka bayar da amincewar amfani da su”. Mr. Osita.

Mr. Osita, tab akin Umar Yakubu ya ci gaba da cewa matsalolin kayyakin marasa inganci a kasuwannin Nijeriya suna da mutukar yawa gaske, a bisa haka ne ma suka bijiro da wannan sabowar alamar domin samar da hanyoyin kawar da munanan kayayyakin da ba su da inganci a Nijeriya “Yanzu muna son kowani dan kasa ya sani, dukkanin lokacin da mutum ya je kasuwa ya daga kayan da zai saya, ya tabbatar ya duba idan ya ga babu wannan sabowar alamar ta PAM to tabbas wannan kayan bai samu sahalewa daga hukumar mu ba, kuma zai iya iyuwa babu inganci a tattare da shi, don haka abu mafi sauki kada ya saya”.

Shugaban ya kuma bayyana cewar akwai dokar da ta ba su damar hukunta dukkanin wadda ya yi biris da dukkanin wani dokar da suka kawo “Muna doka na SON ta 2015 ta ba mu ‘yanci, ta ba mu dama, dukkanin wani wadda ke yin kayan da babu inganci a cikinsa, za mu daukesa mu hukunta shi, mu kuma kaishi kotu da wajen ‘yan sanda, akwai tarar da za a ci a wajensa matukar aka samu mutum na fitar da kayyakin da babu inganci a tattare da su. Don haka za mu tabbatar da wannan sabon tsarin namu kowani mai fitar da kaya a fadin Nijeriya na amfani da shi”. A cewarsa

Dangane da kayyakin da ake shigowa da su cikin Nijeriya daga kasashen waje kuwa, shigaban ya ce “wannan kam ai tun shekaru goma sha bakwai da suka wuce muka kawo wata tsari mai kama da wannan, shi wannan tsarin dukkanin wani kayan da zai shigo, sai an yi gwajinsa an tabbatar da akwai inganci a cikin kayan nan, kafin a ba da izinin shigo da ita, idan kuma muka tabbatar da kayan ba su da inganci za mu kona ko mu maidasu kasashen da suka fito”. A ta bakin Mr. Osita.

Shugaban ya ce, wannan sabon tsari na alamar da za a ke sanyawa wa dukkanin kayyakin amfani zai kawo ci gaba sosai wajen rage gurbatttun kayyaki a Nijeriya.

Shugaban ya ce  a kowani lokaci suna aiki kafada-kafada da hukumomi irin su Custom da kuma NAFDAC domin ci gaba da tsaftace gurbattun kayyaki amgani a Nijeriya.

Da yake karin haske kan banbancin aiki da ke tsakanin SON da NAFDAC ya ce “Muna da banbanci aikin sosai da NAFDAC, su Nafdac suka kula ne da magunguna da kayyakin abinci, suna dubawa, amma su ba su tabbatar da cewar wannan akwai inganci a cikinsa ko babu. sai dai su duba kamar a ce adadin kayyaki, mu kuma muna duba dukkanin kayyaki ne. yanzu kamar irin ruwan leda ko na gora mu muna duba har da girman leda da kuma addireshin wadda ya yi ta, su kuma ruwan da ke ciki kadai suke dubawa. Wannan dalilin ne ya sa ake kiranmu Standards Body, muna kula da abinci da abun da ya rufa abincin”. A cewar shugaban hukumar kula da inganci kayyaki a Nijeriya.

Da take jawabin maraba, Ko’odinatan hukumar kula da ingancin kayyaki a Nijeriya, Injiniya Hauwa Muhammad Hussain ta ce, wannan tambari wato LOGO na PAM da hukumarsu za ta fara amfani da shi, kai tsaye zai dakile yaduwar kayyakin da ba su da inganci a Nijeriya a cewarta hakan zai kara inganta lafiyar jama’an kasa da kuma samar musu da abinci masu gina jiki a kowani lokaci “muna da tsaruka daban-daban na tabbatar da cewar kayyakin da ake sarrafawa a  Nijeriya kuma a  ke saidasu a kasuwanni suna da indanci a kowani lokaci”

Hauwa Hussain ta kara da cewa, “Hatta kayyakin da aka sarrafa su daga waje aka shigo da su, su ma muna bibiyarsu domin tabbatar da cewar suna da inaganci gabanin amfani da su a cikin Nijeriya, har rijista muna yi wa kayyakin kasashen waje”.

Wannan sabon tambarin ta ce dole ne kowani mai sarrafa kaya yake amfani da shi “tilas ne yanzu ne dukkanin wasu kayyakin da za a sarrafa sai suna da wannan tambarin gabanin a saida su a kasuwa. Shi wannan sabon tsarin mai suna ‘PAM’ zai zama wata hanyace ta tabbatar da inganci kayyaki cikin sauki don haka muna kira ga jama’a kowa ya rungumi wannan sabon tsarin domin inganta lafiyar ‘yan kasa”. In ji Injiya Hauwa SON.

Daya daga mahalarta taron, Emmanuel Ikegbo wadda kuma mai saye da sayarwa ne, ya bayyana ra’ayinsa kan wannan sabon tsari na PAM da cewar tabbas za su amshi wannan shirin hanu biyu-biyu, kuma za su mara baya wajen tabbatar da wannan alamin ya yi amfani cikin sauki ba tare da baiwa hukumar wahala ba; haka nan kuma ya ce su kansu sun yi na’am dari bisa dari da wannan tsarin.

Masu jawabi daga hukumar hana fasa kwairi, ‘yan sanda, NAFDAC da Cibil Defences dukkaninsu sun bayyana aniyarsu na bayar da hadin kai domin tabbatuwar wannan sabon tsarin da zai kawo raguwar gurbattun kayyakin amfani a fadin Nijeriya, don haka ne suka kuma nemi jama’an kasa das u mara wa shirin baya don kare kai daga cuttukan da suka jibinci amfani da gurbattun kayyaki a kasuwanmu ta Nijeriya.

 

 

Exit mobile version