KAYAN HADI:
- Alayyahu
- Kwai, Mai
- Tattasai, tarugu, albasa, tafarnuwa.
YADDA ZA A YI: A wanke alayyaho a yayyanka kanana, sai a yay yanka albasa a jajjaga kayan miya. Farko za ki samu tukunyar da babu komai, asa a wuta ki juye alayyahon duka ki dan turara shi. In kina da steamer za ki iya saka shi a ciki ya turaru sai ki sauke.
Ki zuba mai kadan a tukunya ki juye albasa, in yadan soyu sai ki zuba kayan miya, ki zuba seasonings da spices, in ya soyu kijuye alayyahon ki jujjuya su hade.
Ki kada kwai ki juye a ciki ki juya su hade da kyau, in yagama soyuwa sai ki sauke. Za ki iya ci da farar shinkafa, jollof rice, fried rice ko ma do ya da dankali.