SOS DIN ALAYYAHU DA KWAI

KAYAN HADI:

  1. Alayyahu
  2. Kwai, Mai
  3. Tattasai, tarugu, albasa, tafarnuwa.

YADDA ZA A YI: A wanke alayyaho a yayyanka kanana, sai a yay yanka albasa a jajjaga kayan miya. Farko za ki samu tukunyar da babu komai, asa a wuta ki juye alayyahon duka ki dan turara shi. In kina da steamer za ki iya saka shi a ciki ya turaru sai ki sauke.

Ki zuba mai kadan a tukunya ki juye albasa, in yadan soyu sai ki zuba kayan miya, ki zuba seasonings da spices, in ya soyu kijuye alayyahon ki jujjuya su hade.

Ki kada kwai ki juye a ciki ki juya su hade da kyau, in yagama soyuwa sai ki sauke. Za ki iya ci da farar shinkafa, jollof rice, fried rice ko ma do  ya da dankali.

Darasi: Za ki iya zuba isasshen kwai ni na fi son shi a haka. Ba dole sai spinach ba, za ki iya yi da sauran ganyayyaki. Kuma za ki iya yi babu kayan miya, idan ki ka yi steaming alayyahon tare da albasa sai ki kada kwai ki juye a ciki. A kula sosai idan kin yanka alayyaho ne kafin kiyanka to kizuba ruwa isasshe yanda zai taso sama, sai ki kwashe zakiga kasan ya koma kasa, in ba haka baza ki rinka ci ki na jin kasa. Yana da dadi in aka sanya a shin kafa. Ga kuma kara lafiya.

Exit mobile version