Southgate Zai Ci Gaba Da Jan Ragamar Ingila

Southgate

Mai koyarwa Gareth Southgate zai ci gaba da aikin jan ragamar tawagar Ingila, bayan da ya saka hannu kan kwantiragin tsawaita zamansa kuma Southgate ya saka hannu kan yarjejeniyar da za ta kare da hukumar kwallon kafa Ingila zuwa Disambar shekara ta 2024. Kocin wanda kwantiraginsa zai kare a karshen kakar wasa ta 2022 tun farko, bayan gasar cin kofin duniya da za a yi a Katar a shekarar 2022, ya fara aikin horar da Ingila daga watan Nuwambar shekara ta 2016.

Southgate ya kai Ingila wasan karshe a gasar Euro 2020 a watan Yuli – kwazo mafi girma da tawagar ta yi tun bayan shekara 55, shekarar 1966 kenan da kasar ta lashe gasar cin kofin duniya.

Kocin zai kai Ingila gasar kofin duniya da za a yi a 2022 a Katar tsakanin 21 ga watan Nuwamba zuwa 18 ga Disamba da kuma buga wasannin neman shiga gasar nahiyar Turai ta Euro 2024 da za a yi daga 14 ga Yuni zuwa 14 ga Yuli. Haka shi ma mataimaki, Stebe Holland ya amince ya ci gaba da aikin tare da Southgate zuwa karshen kakar 2024 kamar yadda suka fara aikin tare bayan shafe shekara da shekaru suna aiki.

Southgate ya fara karbar aikin a matakin rikon kwarya daga wajen tsohon kociyan Newcastle United Sam Allardyce cikin watan Satumbar shekara ta 2016, sannan wata biyu tsakani aka bashi wuka da nama. Ya kuma kai Ingila karawar dab da karshe a gasar kofin duniya da aka yi
a Rasha a 2018, kuma kokari a karon farko tun bayan shekara 28, sannan a karkashin Southgate Ingila ta yi ta uku a Uefa Nations League, ta kuma kai wasan karshe a Euro 2020 da Italiya ta yi nasara a Wembley, kuma wasan da aka doke tawagar kenan a shekarar.

Tawagar Ingila ta ci wasanni 44 a karawa 68 karkashin jagorancin
Southgate da rashin nasara a wasa 14 da canjaras 10 kuma ana rade radin
cewar kwantiragin da Southgate ya amince har da albashin fam miliyan
biyar zuwa shida a shekara.

Exit mobile version