Connect with us

RAHOTANNI

Soyayya Da Falsafarta a Cikin Al’umma

Published

on

08100407123
kabiruyusuf533@gamail.com
MA’ANAR SOYAYYA
Soyayya wata alakace da Allah (t) ya sa ta a tsakanin jinsin halittarsa ba wai mutane kawai ba, misali;ana soyayya a tsakanin jinsin aljanu da aljanu. haka a tsakanin dabbobi da dabbobi.Ana kuma samunta a  sauran dangogin halittar da ke rayuwa a  Duniya kuma kowanne jinsi akwai siga da yadda ya ke gudanar da soyayyarsa. Allah ya yi hakan ne domin rayuwar halittarsa ta yi ma’ana, ta yadda za su samu sukunin zamanatakewa a tsakaninsu da a ce babu soyayya da rayuwa ba ta yi ma’ana ba sam!
Allah (t) ya shimfida rayuwar halittarsa bisa falsafa (hikima) mai fadin gaske, wanda da a ce babu soyayya tabbas da rayuwa sam ba ta yi dadi ba.tabbas da al’amura sun dagule,da sun yamutse,domin kuwa rayuwar karazubanci wacce  babu soyayya a cikinta ba za ta yi kyawu a tsakanin halittar Allah (t) ba.Da kashe-kashe da tashe-tashen hankula sun kazanta a doron kasa.da kone-kone da asarar dukiyoyi sun mamaye birane da kayyuka a takaice ma, da babu soyayya tabbas da rayuwar halitta sam ba ta yi ma’ana ba.
RABE-RABEN SOYAYYA
Soyayya ta ka su daban-daban kamar yadda muka dan haska a sama kadan a baya.Ga tsakure dangane da hakan-;
1. Akwai soyayya a tsakanin mutane ta yadda Namiji ya ke bayyanawa Mace soyayya har ta kai su ga aure.
2. Akwai soyayya a tsakanin dabbobin  da suke rayuwa a wannan duniyar,su na da salon yadda suke yinta,har ta kai su ga yin zamantakewar rayuwa.
3. Akwai soyayya a tsakanin mutum da abunda ya mallaka.misali;dan adam ya kan bayyana soyayyarsa ga dukiyar da Allah ya mallaka ma sa,haka yana nuna soyayyarsa ga motarsa,gidansa,da duk wani abu da yake rayuwa da shi.Ita ma irin wannan soyayya ta kan budewa Dan adam wata nau’i na jarabawa a rayuwarsa.
4. Soyayyar da dan adam ya ke nunawa ‘ya’yansa,ta yadda zai iya sadaukar da jin dadinsa domin su.haka zai iya zamantowa kyandir din da yake kona kansa domin ya haska mu su rayuwa.Zai iya zamantowa Allurar da zai rika dinka musu kayan sawa,shi kuma ya kasance ba tare da ya yi ado da irin kayan da suka sa ba.Ita ma irin wannan nau’in soyayya tana ciki wacce ta ke wahalar da dan adam,ta ke jefashi cikin dangogin jarabawa a rayuwarsa.Amma insha Allahu a nan zamu dan yi fashin baki ne a dangane da soyayyar da ta ke gudana a tsakanin mutane.
SOYAYYA DA FALFASARTA
Falsafa (tana nufin son hikima) kamar yadda manyan malaman koyar da falsafa  kamar su;dorojaye,Shauhan,Abu jado suka tabbatar. A nan za mu ga cewa;Allah (t) ya sa ka soyayya a tsakanin dukkanin halittarsa domin rayuwar ta yi ma’ana.mu kalli yadda miliyoyin halitta suke nuna zunzurutun kauna g ga Annabi Muhammad (s),wannan yana daga cikin hikimomi da falsafar soyayya a tsakanin mutane.bugu da kari Alkur’ani mai girma ya kissata ma na yadda soyayyar Annabi Yusuf (as) ta mamaye zuciyar matar sarki Zulaihat.Kissar Annabi Yusuf (as) da ta zo a cikin alkur’ani,ta bayyana yadda kaunar Annabi Yusuf (as) ya zamanto jinta,ganinta,barcinta,tashinta,tsayuwarta duk sunanshi ta ke kira,hakan ya sa ta rasa dukkanin kyawun da mai duka ya yi ta da shi saboda tunanin bawan Allah Annabi Yusuf dan Ya’akub (as),amma a sadda ta yi imani da gasken-gaske bayan da ya yi addu’a aka dawo ma ta da kyakykyawar halittarta,sai aka ma sa wahayi akan ya aure ta ya kuma aikata hakan.
A nan za mu ga cewa;soyayya a matakin karshe ita ce ta bawa a tsakaninsa da Allah (t).domin shi ne babban masoyin da bai taba barin masoyinsa a cikin tsanani ba tare da ya tallafa ma sa ba,haka shi ne babban masoyin da ba zai taba kunyata masoyinsa ba dukkanin Annabawa sun riki mahalicccinsu a matsayin babban masoyinsu na karshe, hakan ya sa suka rabauta a duniya da lahira.
Annabi Yusuf (as) yana cewa: “babu wani bala’i da ya sameni sai sakamakon so,babana ya so ni,’yan uwana suka mini hassada,innata ta so ni,har ta dangani da sata,matar sarki ta so ni har ta wurgani a kurkuku”Sayyadina Ali (Rta) yana cewa:”son abu yana makantarwa ya kurumtarwa”3.haka yana cewa:”wanda yake son abu zai yawaita ambatonsa.”(littafin guraril hikam)
Ma’ana ita kanta soyayya tana daya daga cikin jarabawoyin da Allah (t) ya ke yi wa bayinsa domin ya ga juriya da hakurinsu.
YA AKA YI SOYAYYA KE KULLUWA A TSAKANIN MUTANE? Duniyar nazarin halayyar dan adam ta gano cewa;tabbas  Mace ba za ta taba yin rayuwa mai nagarta ba,ba tare da namiji wanda zai zamanto ma ta inuwa da garjin rana, bargon rufa a lokacin da ake suburbuda sanyi ba.a gefe guda shi ma namiji rayuwarsa ta kan zamanto lami-lami idan Mace ba ta shigo cikinta ta ta ba da gudummarta a ciki ba.namiji yana da dabi’a da halayyar gwagwarmaya da gudanar da rayuwarsa cikin karfi da izza ba jure raini,habaici,kallon hadarin kaji,a kan abunda bai taka-kara ya-karya ba,zai iya zare takobi ya shekar da jinin abokin hamayyarsa.a kan abunda bai taka-kara-ya-karya ba,zai iya kona dukiyar dubban nairori.Cikin hikima ta Allah sai ya kaddara shigowar Mace a cikin rayuwarsa domin rayuwar ta sa ta  ta yi ma’ana.A duk sadda ya dawo cikin gida daga wajen sana’arsa ko office cikin fushi a sakamakon hassalashi da wani ya yi a waje,cikin kankanin lokaci Mace za ta iya shawo kansa da ‘yan kalmomin da ba su wuce jumla guda ba.Shi ya sa gawurtattun masana halayen dan adam da zamantakewar aure suke ganin rashin kwazon Matar da ta ka sa amfanin da makaman yakin soyayya domin kawar da hucin da na namiji yake yi a sadda aka hassalashi.ko kuma ta yi yunkurin kwantar ma sa da hankali a sadda tunaninsa ya dunguzuma.
Kowanne jinsin  aan adam Namiji ne ko Mace, yana da dalilansa da suka sanyashi yin soyayya da abokin soyayyarsa,misali;wani zai ga sigar halittar Mace ne sai ya fada cikin komar da ta baza ma sa.wani hazakar Mace ne ke cusa ma sa soyayyarta.wani kuma iya tafiyarta ne ya ribace tunaninsa.Wani kuma iya sa kayanta ne ke zamantowa kanwa-uwar-gamin saukar da shi a kasuwar soyayyarta.Wani kuma zakin lafazinta da tattausar muryar ta ne ya burge shi.Su ma matan makamantan ire-iren wadannan dalilan da muka ambata ke kai su ga fadawa tsundum cikin tekun soyayyar Mace.Wani bincike na masanan halayyar dan adam yana nuna yadda aka samu sabani a tsakanin mutane wajen bayanin abunda ake kira kyawu,domin kuwa kowanne jinsin dan adam Namiji ne ko Mace yana da abunda zai kira kyau a nazarinsa da mahangarsa.Abunda wani zai fassarashi a kyau,wani kuma akasin hakan zai bayyana.Ma’ana kowanne ‘allazi da na sa amanu’.
Advertisement

labarai