Soyinka Ga ‘Yan Nijeriya: Ku Yi Hankali Da Gamayyar Makiya Dimokuradiyya

Daga Umar A Hunkuyi

Sanannen marubucin nan, Farfesa Wole Soyinka, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su sa ido sosai su kuma yi taka-tsantsan da gamayyar mutanan da ya kira da makiya Dimokuradiyya.

LEADERSHIP A YAU, ta kawo rahoton cewa, kwanan nan tsohon Shugaban kasannan, Cif Olusegun Obasanjo, ya kafa wata kungiyar gamayya wacce ya kira da cewa, ita ce za ta ceci Nijeriya daga halin da take ciki yanzun.

Da yake magana wajen taro na 80 na bukin tunawa da shahararren mai rajin kare hakkin dan adam din nan, Cif Gani Fawehinmi, a Ikeja, Legas, ranar Lahadi, Soyinka, cewa ya yi, tilas ne ‘yan Nijeriya su sa ido sosai don kuwa Dimokuradiyyan kasarnan tana cikin hadari.

Taken bukin na bana shi ne, “Dimokuradiyya abin dogaron talakawa, ta hanyar kyakyawan shugabanci.”

A cewar Soyinka, “Abin da kawai zan ce maku kan taken wannan taron shi ne, ku sa ido sosai, a cikin al’ummar nan tamu kamar sauran al’ummu, akwai mutanan da da zaran sun hangi wata matsala, nan da nan sai su taru tamkar tamkar taruwan angulaye. Tabbas taken wannan taron ya dace, kuma tabbas Dimokuradiyya tana cikin hadari. Ba ma kawai Dimokuradiyyan kasar ba, al’ummar ma tana cikin hadari.

“Tambayar a nan ita ce, shin hakan dama ce a gare mu na mu yi aikin ceto, ko kuwa dama ce a gare mu na mu sake amfani da hakan wajen ci gaba da abin da muke yi, na taimakawa wajen kara durkusar da kasar?

“Ina da tabbacin wadanda suka mayar da kansu, makiyan Dimokuradiyya, wadanda su suka kirkiri halin da ake ciki, sun fitar da wasu tsare-tsaren da su ne suka jaza mana halin da muke ciki a yau, yanzun kuma sun sake dawowa sun shirya kawukansu a matsayin wai sune masu ceto.

A nan dai,Soyinka,yana magana ne kan Obasanjo da kungiyar gamayyar nan na shi, inda yake cewa, kungiyar gamayyar tana kokarin nu na kanta a matsayin wai ita ce mai ceton nan da Nijeriya ke fatan samu. Abin ya ba ni mamaki, saboda a farkon wannan gamayyar akwai kungiyoyi biyu da suka hadu da sunaye mabambanta. Cikin su akwai mutanan da nake ganin na kirki ne da a iya bin su, a ma kira wasu da su bi su.

“Amma kwatsam, sai na ga wasu mutanen da su ne suka fara kafa tushen rugujewar Dimokuradiyya sun mamaye tafiyar. Kawai sai muka ji cewa, wai suna ta shirya yin gangamin gamayya. Daya daga cikin su ya taba kira na, wai na zo na yi masu jawabi. Tambayar da na yi masu ita ce, ko daman su ne suka fari wannan tafiyar, daga nan na gaya masu ka da su sake matsowa inda nake. Matukar ka shiga cikin su, ka zama daya daga cikin makiya Dimokuradiyya a kasarnan.

“Su ne suka kafa wai abin da suka kira da, gyaran tsarin mulki, zancen banza kawai, sun so hakan ne domin su sami daman ci gaba da shirin na su, wanda tuni ya watse, wanda aka sani da tsawaita lokacin zama a kujerar mulki, abin da ya kusa tsiyata asusun kasarnan kaf.”

“Yanzun kuma wai sai ga shi sun zo suna shirya tarukan gamayya a ko’ina, domin su rikita mutane, musamman shugabannin kirkin da zamu iya aminta da su. Amsan hakan mai sauki ce. Kamata ya yi ka duba tarihin su na baya. Ka da ka yarda ka jefa kanka cikin ciwon dimuwa, da zai sa ka manta da gaskiyan abin da ya faru a baya.

“Mun yi Shugaban kasan da a kasarnan ya nemi zama babban azzalumin da kasarnan ta taba sani. Mun kuma yi wasu shugabannin da suka yi komai wajen ruguza mulkin Dimokuradiyya. Kuma suna kiran kansu, mutanan da Allah ya sanya nemowa kasarnan mafita.

“Kawai kuma sai na ga mutane su na ta binsu. Har su na neman su da su sake mulkan su. Ko da ba su fito a fili ba, amma dai su din ne, suna ta gyara hanyar na su, ‘yan koren su na yi masu aiki. Ina kiran mutane da su yi hattara.

Shi ma da yake jawabi a wajen taron, Lauyan nan mai rajin kare hakkin dan adam, Femi Falana, kiran ‘yan Nijeriya ya yi da su yi taka-tsantsan ka da su bari mutanan da suka rusa kasarnan su dawo suna cewa su ne za su ceci kasar.

“Wannan mutumin fa ya shugabanci kasarnan shekaru 11 da rabi, in an hada da shugabancin da ya yi zamanin mulkin sa na Soja. Ya so ya yi tazarce a karo na uku kafin shirin ya watse. Yanzun kuma ya zo yana cewa wai ya san mafitar matsalolin kasarnan.

“Wannan ne ya sanya nake tambayar sa da ya mabata mana ko da daya daga cikin matsalolin kasarnan da ya magance. Ya kashe dala bilyan 16 wajen jefa kasarnan cikin duhun rashin hasken lantarki. Wannan mutumin ya mayar da dukiyar kasar na shi. Nijeriya ce kadai kasar da Shugabanta da mataimakin sa suka kafa Jami’o’in su, suka kuma yi watsi da Jami’o’in al’umma.”

Wani dan Majalisa, Sanata Shehu Sani, cewa ya yi, kasarnan ta fita daga mulkin Soja, amma har yanzun ba ta dandani Dimokuradiyya ba, ya kara da cewa, “kasarmu fa ba ta da lafiya” domin a kullum kuma a ko’ina fa mutane ne ke mutuwa wasu kuma ana ta kashe su.

Sanata Sani ya ce, duk da cewa, kasarnan ta rabu da mulkin danniya irin na PDP, amma dai har yanzun ba ta kai ga gaci ba, ya kara da cewa, wadanda suka bata kasar sun sake dawowa, kamar wasu mutanan kirki, sai ya umurci ‘yan Nijeriya da ka da su kuskura su zabi Jam’iyya, sai dai mutanan da suka cancanta.

Exit mobile version