Kungiyar manyan ma’aikatan jami’o’in Nijeriya (SSANU) da kungiyar ma’aikatan ilimi (NASU) sun shirya kaddamar da zanga-zangar kwana daya a fadin kasar a ranar Alhamis, 9 ga watan Oktoba, kan gazawar gwamnatin tarayya wajen magance matsalolin da suka dade suna bukatar gwamnatin ta warware.
Sanarwar ta biyo bayan wani cikakken nazari da kwamitin hadin gwiwa na kungiyar (JAC) ya yi a ranar 6 ga watan Oktoba, bayan karewar wa’adin da aka bai wa gwamnati.
A wata takardar da aka mika wa daukacin shugabannin NASU da SSANU na jami’o’i da cibiyoyin jami’o’i mai taken “Ƙaddamar da zanga-zanga”, JAC ta umurci dukkanin rassa da su gudanar da taron gaggawa a ranar Laraba domin zaburar da ‘ya’yan kungiyar don gudanar da ayyukan zanga-zanga a harabar jami’o’i. A yayin zanga-zangar, za a yi rubuce-rubuce a alluna, da taron manema labarai don bayyana kokensu a bainar jama’a.
Takardar mai kwanan watan Oktoba 6, ta samu sa hannun Prince Peters Adeyemi, babban sakataren NASU, da Comrade Mohammed Ibrahim, shugaban SSANU na kasa.