Muhammad Auwal Umar" />

Stars Foundation Ta Tallafawa Marasa Karfi 300 A Neja

Taimakon jama’a ba sai ka rika matsayi mai karfi, domin tausayi na cikin zuciya ne da irin wannan yanayin ne kadai mutum zai iya anfani da dan abinda ke hannunsa wajen jinkan marasa karfi, Hajiya Habiba Inuwa wata dattijiya ‘yar kimanin shekaru hamsin da uku da ta samu tallafin abinci daga gidauniyar Stars Foundition ta bayyana hakan a lokacin da ta ke bayanin godiya a madadin dattijai maza da mata da Iyayen marayu da suka samu tallafin.
Hajiya Habiba tace lallai wannan gidauniyar ta shahara wajen koyar da mata da ‘yan mata sana’o’in hannu wanda da daman matan aure da ‘yan mata sun anfana suna sarrafawa a siya koda a cikin gidaje ne. Saboda ta jawo hankalin masu hannu da shuni da su dauki irin wannan salon wanda zai taimaka gaya wajen rage radadin talauci da rashin aiki da ke addabar matan karkara da na birni, wanda da zaran mace ta samu sana’a kasancewarta uwa za ta iya samun wata hanya da zai dakile mata wasu ‘yan matsalolin cikin gida.
Hajiya Aishatu Tukura Bmibtasahe, uwargidan shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jiha, ta yaba da irin wannan yanayi da kuma hubbasan da shugabar gidauniyar ta mayar da hankali wajen taimakawa, tace wannan wani gibi ne ake cikewa gwamnati musamman na samar da ayyukan yi ga marasa aiki ko bada taimako ga wanda aka fuskanci yana bukatar hakan, domin da masu hannu da shuni da sauran wadanda Allah ya dan yiwa falala zasu rika duba na kasa da su, ina da tabbacin da mutane sun samu walwala koda ba su iya tara kudi mai yawa ba.
“Ina jawo hankalin wadanda aka horar aka taimaka masu da dattijai masu rauni zasu yi anfani da abubuwan da aka ba su dan yin anfani da shi yadda ya kamata, ya zama su wadanda aka horar kar su dauka abu ne na siyasa, wannan wata muhimmiyar dama ce suka samu wanda zai taimaka masu su iya rike rayuwarsu.”.
Tallafin gidauniyar dai wanda mutane dari uku maza da mata suka anfana sun kunshi maza dattijai goma sha daya, mata da ke goyon marayu su ashirin da biyar da kuma da zama a mazabar Ciroma da ke zaune a Tudun Wada ta Kudu da cikin karamar hukumar chanchanga, da ta ke bayani ga din bin jama’ar da suka anfana da shirin, babbar bakuwar a taron Hajiya Aishatu Bhmitosahe tace wadanda suka anfana da shirin da su rike wannan sana’ar da suka koya hannu biyu domin zai iya taimaka masu a rayuwa na kaiwa ga wani gaci a rayuwa, duk wani dan kasuwa ya zama wani abu yau ya fara ne daga kadan wanda ya kai shi a wannan matsayi.
Da ta ke zantawa da manema labarai bayan kammala taron, Hajiya Zara I. Abdullahi tace wannan ba shi ne karon farko da gidauniyar ta tai irin wannan shirin ba, wannan ya bambamta da na baya ne domin mun bada tallafin abinci ga masu rauni da kuma kayan kula da kiwon lafiya, sannan duk da cewar gidauniyar ba ta siyasa ba ce amma na yi la’akari da gudunmawar da maigirma gwamna Abubakar Sani Bello ya baiwa rayuwar mata, yasa na zakulo mata daga mazabu ta Ciroma a Tudun Wada south na horar da su da kuma ba su tallafi da takardar shaidar koyon sana’a dan nuna godiyar mu ga kudurin uwargidan gwamna, Hajiya Amina Abubakar Sani Bello na inganta rayuwar mata.
Saboda haka Stars Foundations za ta cigaba da irin wannan a duk lokacin da bukatar hakan ta taso, idan gwamnati tayi rawar gani zamu fito mu mara mata baya, dan haka a matsayin mu na mata zamu cigaba da nuna goyon bayan ga gwamnatin jiha saboda manufofin mu ya zo iri daya da na ta wajen inganta rayuwar jama’a da samar da kyakkyawan yanayin da zai iya baiwa kowa damar dogaro da kan shi.
Taron dai ya samu halartar shugaban kungiyoyi masu zaman kansu, da manyan mata ‘yan siyasa sun yaba da irin jajircewar wannan gidauniyar na inganta rayuwar mata da masu rauni.

Exit mobile version