Stones Zai Yi Jinyar Makonni Shida

Mai koyar da yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, Pep Guardiola ya bayyana cewa dan wasan kungiyar, John Stones dan kasar ingila zai yi jinyar mako 6 bayan yaji rauni a cinyarsa a wasan da kungiyar tasamu nasara akan Leceister City daci 2-0 a wasan firimiya mako na 12.

Guardiola ya ce abin bakin cikine da takaici ga kungiyar da kuma dan wasan domin zai dade bai buga wasa ba kuma kungiyar za ta yi rashinsa.

Ya ci gaba da cewa duk da cewa basu day an wasan baya da yawa amma yasan yan wasansa zasuyi kokarin ganin sun cike gurbin Stones.

Dan wasan dai ya bugawa Manchester City wasanni 18 a wannan kakar kuma ya zura kwallaye uku kawo yanzu inda ya taimakawa kungiyar a yanzu take mataki na daya akan teburin gasar firimiya maki takwas tsakaninta da Manchester United United wadda take matsayi na biyu.

Exit mobile version