Daga Ahmed Muh’d Danasabe, Lokoja
Ranar Lahadi da ta gabata ne garin Ankpa dake Jihar Kogi ya cika makil da jama’a, inda mashahuran mutane ciki har da ’yan siyasa suka hallara a garin, domin halartar sadaka da addu’ar kwana arba’in da rasuwar mahaifiyar sananniyar ’yar siyasar nan, Hajiya Halima Alfa, wato Marigayiya Hajiya Hauwa Kadiri.
Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Sanata Kabir Ibrahim Gaya, da mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Kogi Hon Muhammed Muhammed suna daga cikin wadanda suka halarci Addu’ar.
Babban limamin garin Ankpa kuma shugaban majalisar malamai na jihar Kogi, Sheikh Salman Adam, wanda ya jagoranci addu’ar, ya karanto wasu surori daga cikin Alkur’ani mai tsarki da Hadisi, inda ya roki Allah (SWT) da ya gafarta wa Marigayiya Hajiya Hauwa Kadiri da kuma yi mata Addu’ar samun rahamar Allah.
Wakilimmu ya ruwaito cewa maigidan Hajiya Halima Alfa, kuma dan majalisa mai wakiltar Kano ta Kudu, Sanata Kabir Ibrahim Gaya da yayansa, wato Tukur Kabir Gaya da Faisal Kabir Gaya da kuma tsohon shugaban karamar hukumar Ijumu, Barista Fadile sun halarci Addu’ar.
Da yake jawabi ga manema labarai kadan bayan gudanar da Addu’ar, Sanata Kabir Ibrahim Gaya, ya bayyana marigayiya Hajiya Hauwa Kadiri a matsayin mutumiyar kirki wacce tayi rayuwa abin koyi.
Ya ce rasuwar Hajiya Hauwa Kadiri, babban rashi ne ga iyalan gidan Eneojo da kuma garin Ankpa baki daya.
A don haka yayi Addu’ar Allah ya yafe mata kurakuranki da kuma saka mata da Aljanna Firdausi.
Addu’ar kwana 40 na marigayiya Hajiya Hauwa Kadiri, wanda aka gudanar a harabar gidan iyalan Eneojo dake garin Ankpa a jihar Kogi, ya samu tubarrakin shugaban karamar hukumar Ankpa, Hon Ibrahim Abagwu da Katukan Lokoja, Hon Bala Salisu da sarakunan gargajiya da kuma ’yan siyasa.