Abba Ibrahim Wada" />

Su Wa Su Ka Fi Cin Kwallo A Firimiyar Nijeriya Wannan Kakar?

Gasar firimiyar Nigeriya tana daya daga cikin manyan gasanni a nahiyar Africa masu wahala sannan kuma tana daya daga cikin gasar da take fitar da zakakuran ‘yan wasan da suke bugawa tawagar Super Eagles ta Nigeriya wasa.

Kawo yanzu, dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Akwa United, Ndifreke Effiong shi ne kan gaba a cin kwallaye a gasar Firimiya Najeriya bayan da a karshen mako aka yi fafatawar sati na 21, kuma kawo yanzu Effiong yana da kwallaye 10 a raga.

Dan wasa na biyu wanda ya ke bin sa a baya shi ne Victor Mbaoma na kungiyar kwallon kafa ta Enyimba International, inda ya ci kwallaye guda tara, shi ne na biyu a jerin wadanda ke kan gaba a cin kwallo a gasar.

‘Yan wasa uku ne ke kan-kan-kan da suka zura kwallaye guda takwas-takwas a raga kowannensu da ya hada da Tasi’u Lawan na Katsina United sai ragowar da suka hada da Ibrahin Mustapha na  Plateau United da Israel Abia na Rangers International.

Bayan buga wasannin mako na 21, Plateau United tana a mataki na daya da makinta 37 sannan kungiyar kwallon kafa ta Ribers United ta biyu da maki 36, sai Lobi Stars ta uku wadda ita ma makinta 36.

 

Sakamakon wasannin mako na 21:

Jigawa Golden Stars 2-1 Wikki Tourists

Lobi Stars 0-0 Plateau United

Akwa United 1-1 Warri Wolbes

Ribers United 2-1 Kano Pillars

MFM 0-0 Heartland

Adamawa United 2-1 FC Ifeanyiubah

Sunshine Stars 0-0 Rangers

Katsina United 1-0 Abia Warriors

Nasarawa United 2-0 Enyimba

 

Wasannin mako na 22 da za a buga ranar 1 ga watan Maris

Kwara United da Lobi Stars

Plateau United da Jigawa Golden Stars

Heartland da Ribers United

Kano Pillars da Dakkada

Rangers da Adamawa United

FC Ifeanyi Ubah da MFM

Abia Warriors da Akwa United

Warri Wolbes da Sunshine Stars

Wikki Tourist da Nasarawa United.

Exit mobile version